Lakurawa ne suka dasa bom a Zamfara —’Yan sanda
’Yan sanda sun bayyana cewa mayaƙan Lakurawa ne suka dasa bama-baman da suka halaka matafiya a yankin Ɗansadau da ake Jihar Zamfara
Mayaƙan Lakurawa ne suka dasa bom ɗin da ya halaka matafiya a yankin Ɗansadau Jihar Zamfara, cewar rundunar ’yan sanda.
Aminiya ta ruwaito wasu majiyoyi cewa sau biyu bama-baman ɗin da ake zargin ’yan ta’adda ne suka dasa, sun halaka matafiya aƙalla 12 a jihar.
Sau biyu a cikin makon da muke ciki irin hakan ta faru a yankin Ƙaramar Hukumar Maru da ake jihar.
Na ƙarshe shi ne wanda majiyar ta ce ya yi ajalin fasanjoji 12 a wata motar haya da ke tafiya a ƙauyen ’Yar Tasha a kan hanyar zuwa yankin Ɗansadau a safiyar ranar Laraba.
- Kotu ta yanke wa miji da mata hukuncin rataya a Jigawa
- NAJERIYA A YAU: ‘Karambanin’ Malamai kan ƙudurorin Harajin Tinubu
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar wa Aminiya da harin ta wayar tarho, amma ya ce mutum guda ne ya rasu, a yayin da wasu uku suka samu raunuka bayan motar ta bi ta kan abin fashewan da aka dasa a ƙarƙashin wata gada.
Dalijan ya ce, “binciken farko ya gano cewa Lakurawa da sojoji suke fatattaka daga Nijeriya ne suka dasa bom ɗin. Yanzu so suke su tsere daga. Zamfara zuwa Birnin Gwari saboda rakura musu da jami’an tsaro suka yi.
“Amma za mu riske su mu gama da su, a in da muke so daga jama’a shi ne su taimaka mana da bayanai kan motsin ’yan ta’addan.”
A ranar Lahadi wani bom ya tashi a ƙauyen Mai-Gungume, ya yi ajalin wani direban motar haya.
Wani mazaunin yankin ’Yar Tasha da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce, “kwnanan nan muka yi aikin gayya a kan hanyar, amma kuma ’yan ta’adda suka yi amfani da damar suka dasa abubuwan fashewa a daya daga cikin ramukan da muka cike.
“An kai mutanen da abin ya ritsa da su Babban Asibitin Ɗansadau, amma babu wanda a zai iya tabbatar da adadin mamatan. Sannan an girke jami’an tsaro a wurin da abin ya faru.
“Da alamar ’yan ta’adan sun sauya salo musamman a yankin Ɗansadau, domin wannan shi ne harin bom ba biyu da suka kai a cikin mako guda.”
Mazaunan yankunan dai sun roƙi gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai domin kawo ƙarshen matsalar.”