Lakurawa: Sabuwar ƙungiyar ta’adda ta ɓulla a jihohin Kebbi da Sakkwato

Rundunar Sojin Nijeriya ta kuma ayyana neman wasu ƙasurguman ’yan ta’adda guda 9 ruwa a jallo.

Lakurawa: Sabuwar ƙungiyar ta’adda ta ɓulla a jihohin Kebbi da Sakkwato

Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta’adda mai suna Lakurawa a jihohin Sakkwato da Kebbi, da ke zama babban ƙalubalen ga sha’anin tsaro a Arewa maso Yammacin ƙasar.

Rundunar ta kuma ayyana wasu ƙasurguman ’yan ta’adda guda tara da take nema ruwa a jallo, tana mai cewa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin ta yi maganin su cikin ƙanƙanin lokaci.

Daraktan Sadarwa na Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Manjo-Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Sakkwato ta yi ƙorafin cewa wata sabuwar ƙungiyar ta’adda ta bulla a jihar.

Kazalika, mazauna ƙauyukan Jihar Borno sun soma bayyana fargabar kwararowar ’yan ta’adda a yayin da dakarun sojin ƙasar Chadi ke ci gaba da tsananta ayyukan kakkaɓe mayaƙan Boko Haram a gaɓar Tafkin Chadi.

Da yake bayani, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce mayaƙan sabuwar ƙungiyar suna kwararowa ne jihohin Sakkwato da Kebbi daga wasu sassa na ƙasar Nijar da kuma Mali tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, lamarin da ya gurgunta alaƙar soji tsakanin ƙasashen.

Sai dai ya bayyana cewa, gabanin juyin mulkin da sojoji suka yi, akwai kyakkyawar alaƙata tsananta tsaro tsakanin jami’an tsaro a iyakokin ƙasashen Najeriya da maƙwabciyarta Nijar.

Ya bayyana damuwa bisa yadda ’yan ta’addan ke ribatar wannan rashin kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

Manjo-Janar Buba ya kuma ƙara da cewa mazauna sun yi wa ’yan ta’addan karamci da matsugunni sakamakon kyautata musu zato da suka yi gabanin gano mugunyar nifaƙar da suke da ita.

Buba ya ba da tabbacin cewa sojoji na ci gaba da tattara bayanan sirri domin daƙile duk wani yunƙurin na ’yan ta’addan, yana mai cewa kwanakinsu a doron ƙasa ƙayyadaddu ne.

Haka kuma, ya bayyana sunayen wasu daga cikin ’yan ta’addan da suke nema ruwa a jallo da suka haɗa da Abu Khadijah da Abdulrahman da Dadi Gumba da Usman Kanin Shehu da Abu Yusuf da sauransu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos