Lakurawa na da jirgi mara matuki, sun karɓe iko a kauyukan Kebbi —Bukarti

Bukarti ya bayyana cewa mayaƙan Lakurawa sun kai shekara shida a Nijeriya kuma a halin yanzu sun karɓe ayyukan sarakunan gargajiya a yankunan Jihar Kebbi

Lakurawa na da jirgi mara matuki, sun karɓe iko a kauyukan Kebbi —Bukarti

Barista Bulama Bukarti

Lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Abdu Bulama Bukarti, ya bayyana cewa Mayaƙan Lakurawa suna kafa manyan sansanoni a yankunan da suka kwace iko a Jihar Kebbi.

Bulama Bukarti wanda ya ce mayakan kasar wajen sun ƙwace aikin sarakunan gargajiya ya bayyana cewa sun kai shekaru shida a Nijeriya kuma suna da haɗari domin akidarsu daya da ta Boko Haram, da ISWAP

Ya ce, “Suna gina manyan sansanoni kuma da mukkan makamai kuma har da jirage marasa matuki da suke amfani da su wajen yin sintiri a kan kauyuka da sansanonin sojin gwamnati.

“Ya kamata a mayar da hankali a yi abin da ya kamata kan wannan lamari, domin ina tsoron nan ba da jimawa ba, za su sama babbar barazanar tsaro.”

Ya ce bayyana cewa “babu ƙaramar hukumar Jihar Kebbi da babu Lakurwa, inda karɓe iko a ƙauyukan da ke wajen hedikwatar ƙananan hukumomin.

“Da wuya ka iya yin tafiyar kilomita biyar ba tare da haɗu da su ba.”

Sai dai ya bayyana cewa, duk da haka, “ba su kai Boko Haram haɗari ba, da barazanar kisa.

Ya bayyana hakan ne a yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar talabijin na Channels.

Bukarti ya ci gaba da cewa, “yanzu haka, Lakurawa ke wa mazauna waɗannan wurare alƙalanci. Idan mutane sun samu saɓani ko rikicin maƙwabta, wurinsu ake kai ƙara saboda sun haramta wa sarakunan gargajiya sanya baki kan duk rikicin da aka kawo musu.

“Sarakunan ba su da zaɓi face su bi, saboda idan suka bijire wa umarnin za su rasa ransu.

“Idan makiyaya suka shiga gonakin manoma da dabbobi, wurin Lakurawa masu gonakin ke kai ƙara. Su za kira mutanen su sasanta su kuma sa a biya wanda aka yi wa ɓarnar diyya.”

Ya ce, “Haka Boko Haram ta bunƙasa ta zama ƙungiyar ta’addanci ta ƙasa da ƙasa. Ba a ɗauki mataki ba, sai bayan da ta shafe shekaru tana gudanar da harkokinta. Ga shi ta samu ƙwarewa ta tara makamai da kuɗaɗen da hanyar garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci.

Da yake magana a yayin zantawar, kakakin Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) Farfesa Tukur Muhammed Baba, ya ce Lakurawa babban barazana ne ga tsaron kasar Nijeriya, muamman yadda suke kokarin kafa sabbin dokoki daban da na gwamnati a yankunan.

Farfesa Tukur ya ce, “Ina magana da shugabannin yankunan, wannan babbar barazanar tsaro ce, suna so su kafa dokoki sabanin na gwamnati.

“Ba za mu yarda ba, idan Shari’ar Musulunci suke magana, ai Jihar Sakkwato ta shafe shekaru tana shari’ar Musulunci. Amma waddanan mutanen ba shari’ar Musulunci suke yi ba.

“Sunan sasanta tsakani sun kirkiro sabbin dokokin kasuwanci, abin tsoro shi ne nan gaba suna iya bullo da sabbin abubuwa kamar rufe makarantu da asibitoci.”