Lakurawa sun kashe fararen hula 20 a Kebbi

A cewar rahoton, akwai yiyuwar ƙungiyar ta kai harin ne domin nuna cewa har yanzu tana da ƙarfin gudanar da manyan hare-hare duk da matsin lambar da hare-haren soji ke yi mata.

Lakurawa sun kashe fararen hula 20 a Kebbi

Mayaƙan Lakurawa sun hallaka aƙalla mutum 20 a wani har a ƙauyen Fesken Rafi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa ta Jihar Kebbi kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Rahotannin sirri da aka tanada domin Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani, ne ya bayyana hakan.

Ko da yake rahotannin kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun nuna cewa harin ya faru ne kwanaki kaɗan da suka gabata, amma lamarin ya fito fili ne a ƙarshen mako bayan Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi ya kai ziyara yankin. Duk da haka ba a bayyana takamaiman ranar da harin ya faru ba.

AFP ta ce ƙoƙarin jin ta bakin jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro bai yi nasara ba.

Rahoton ya ce harin ya zo ne bayan watanni da aka samu sauƙin hare-haren Lakurawa, lamarin da ya sake tayar da hankalin jama’a kan yiwuwar sake ƙaruwa da ayyukan ta’addanci na ƙungiyar.

A cewar rahoton, akwai yiyuwar ƙungiyar ta kai harin ne domin nuna cewa har yanzu tana da ƙarfin gudanar da manyan hare-hare duk da matsin lambar da hare-haren soji ke yi mata.

Rahoton ya tunatar da cewa a ranar 25 ga Disamba, sojojin Amurka sun kai hare-hare a wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya, inda gwamnatin Najeriya ta ce an kai su ne kan mayaƙan ƙungiyar IS, Lakurawa da kuma ƙungiyoyin ’yan bindiga.

Ko da yake ba a san adadin mayaƙan da aka kashe ba, Amurka ta ce hare-haren sun hallaka mayaƙa da dama, yayin da hukumomin Najeriya suka ce ayyukan soji sun raunana ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Har yanzu ba a gano dalilin kai sabon harin ba.

Sai dai a baya-bayan nan, ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ’yan bindiga masu satar mutane da dabbobi sun ƙara kai hare-hare da kuma yin garkuwa da manoman da suka ƙi biyan harajin da suke laftawa al’ummomi kafin a ba su damar noma gonakinsu a yankunan Arewa a Najeriya.

Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na fatattakar su, ƙungiyar Lakurawa na ci gaba da gudanar da ayyukanta a yankunan da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

Rahoton ya yi gargaɗin cewa ayyukan Lakurawa na iya rikiɗewa zuwa barazana ta ƙasashe da dama saboda kasancewar mayaƙanta daga ƙasashe daban-daban, lamarin da ke ƙara wahalar da aikin yaƙi da ta’addanci.

Wasu masu bincike na danganta Lakurawa da ƙungiyar Daular Musulunci ta Sahel, wadda ta fi yin aiki a Mali da maƙwabciyarta Nijar, duk da cewa wasu masana na da shakku kan hakan.

Jami’an yankin sun ce mayaƙan Lakurawa, waɗanda suka samo asali daga Mali da Nijar da Burkina Faso, sun shiga Najeriya tun a shekarar 2018, inda suka kafa sansanoni a jihohin Kebbi da Sakkwato, amma suka fara fitowa fili sosai a shekarar 2023.

Rahotanni sun ce mayaƙan sun kafa sansanoni a Dajin Tsauni da ke kan iyakar Nijar, inda suke kai hare-hare, satar dabbobi da kuma karɓar haraji daga al’ummomi.

A watan da ya gabata, mayaƙan Lakurawa sun kashe sojojin Najeriya bakwai a wani kwanton ɓauna da suka yi musu a Jihar Sakkwato kusa da iyakar Nijar, kamar yadda majiyoyin soji da na yankin suka bayyana.

Tun daga shekarar 2009, rikicin masu tayar da ƙayar baya da Boko Haram da  ISWAP ke jagoranta ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyin jama’a da matsugunansu a Najeriya.