Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Sai dai an samu mabanbantan rahotanni kan haƙiƙanin waɗanda aka kashe.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Mako guda bayan kashe jami’an ’yan sanda biyu, ’yan ta’addan Lakurawa sun sake kai hari, tare da kashe ma’aikatan kamfanin Airtel uku a Jihar Kebbi.

Harin ya faru ne a wajen  gina wani katafaren ƙarfen sadarwa da ke ƙauyen Gumki, a jihar.

Rahotanni sun ce waɗanda abin ya shafa sun girka turakun Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa a lokacin da ’yan ta’addan suka kai farmaki.

Sun kashe su tare da wani mutum guda ɗaya wanda ba a tabbatar da sunansa ba.

Bayanai sun sha bamban kan waɗanda abin ya shafa, yayin da wasu mazauna ƙauyen suka ce ma’aikatan Hukumar Shige da Fice ne aka kashe.

Sai dai ’yan sanda sun tabbatar cewa ma’aikatan kamfanin Airtel ne aka kashe.

Wani ma’aikacin Asibitin Ƙwararru na Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, inda aka kai gawarwakin, ya ce waɗanda aka kashe duk ma’aikatan Hukumar Shige da Fice ne.

Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan, SP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da cewa mutum huɗu ne aka kashe – ma’aikatan Airtel uku da kuma wani mutumin guda ɗaya.

Bayan faruwar lamarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M. Sani, tare da Kwanturolan Hukumar Shige da Fice, Muhammad Bashir Lawali, sun kai ziyara wajen da abin ya faru domin tantance al’amuran tare da ɗaukar gawarwakin zuwa asibiti.

Rundunar ta ƙara tura jami’anta na musamman zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.

Sun kuma roƙi al’ummar yankin da su riƙa bayar da sahihan bayanai domin daƙile irin hakan a gaba.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi