Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi

Mayaƙan kai sabon hari a yayin da mazauna yankin Hukuma suke tsaka da barci

Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi

Mayaƙan Lakurawa sun kashe farar hula ɗaya tare da jikkata wasu shida a yankin Gulma da ke Karamar Hukumar Argungua Jihar Kebbi.

Da misalin ƙarfe 11 na dare ne maharan suka suka wa yankin yayin da mazauna suke tsaka da barci a ranar Alhamis suna harbe harbe-harbe.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, ya bayyana cewa waɗanda maharan suka yi raunin harbi suna samun kulawa a Asibitin Tarayya da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi

’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike

Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno