Lakurawa sun kashe sojoji 6 a Sakkwato
Wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa wani hafsan soja mai muƙamin Laftanar na cikin waɗanda suka kwanta dama.
Sojojin Najeriya a bakin aiki
Sojoji bakwai da farar hula ɗaya sun mutu a wani harin kwanton ɓauna da Lakurawa suka kai a ƙauyen Runji da ke Ƙaramar Hukumar Illela ta Jihar Sakkwato.
Wani babban jami’in soja ya tabbatar wa wakilinmu cewa sojoji shida sun kwanta dama a harin.
Amma mazaunin garin Illela ya shaida wa wakilinmu cewa “Gawarwakin sojoji shida muka gani a wurin, washegari kuma muka aka ga wata gawar soja.”
Wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa wani hafsan soja mai muƙamin Laftanar na cikin waɗanda suka kwanta dama.
Shaidu sun ce sojojin suna dawowa ne a cikin motoci uku, kuma ana kyautata zaton sun ragarji ’yan ta’addar Lakurawa da dama.
- ’Yan ta’adda sun kashe mutum 10 a kasuwa a Katsina
- Sabon harin Amurka da Najeriya ya kashe mayakan ISWAP 20 a Borno
Wata majiya ta bayyana cewa a hanyar sojojin ta komawa zuwa Illela ne motarsu ta lalace, inda wasu daga cikinsu suka tsaya domin gyara ta a bakin titin.
“’Yan ta’adda sun taru suka bi sawun sojojin domin ɗaukar fansa kan ɓarnar da sojoji suka yi musu,” a cewarsa.
Ta bayyana cewa maharan a kan babura kusan 30, kowanne ɗauke da mutum uku, “Sun iske sojojin suna gyaran motar, a nan ne aka yi ƙazamin faɗa na tsawon lokaci a tsakaninsu.”
Wata majiya ta ce sojoji bakwai da wani farar hula ne aka kashe a harin kwanton ɓaunar.
Ta bayyana cewa, “Sojojin sun bar motar suna takawa zuwa sansaninsu tare da wani farin hula da ya san hanyar ne, Lakurawa suka kai musu hari, suka kashe sojoji bakwai da ɗan jagoran nasu,” in ji shi.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa an kai gawarwakin sojojin zuwa Sakkwato.
Wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa wani hafsan soja mai muƙamin Laftanar na cikin waɗanda suka kwanta dama.
Sai dai kuma kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, da kuma Mashawarcin Gwamnan jihar Sakkwato, Kanar Ahmed Usman, ba su amsa tambayar wakilinmu kan harin.
Wani babban jami’in soja ya tabbatar wa wakilinmu cewa sojoji shida sun kwanta dama a harin.