Lakurawa sun tsere bayan sojoji sun ragargaje su a Kebbi
Mayaƙan Lakurawa sun arce daga yankin Jihar Kebbi bayan sojoji sun yi musu luguden wuta.
Mayaƙan Lakurawa sun tsere daga yankin Jihar Kebbi bayan sojoji sun yi musu luguden wuta.
Sojojin sun ragargaji Lakurawan ne kwanaki kaɗan bayan mayaƙan ƙasashen wajen sun halaka mutum 17 a garin Mera da ke Karamar Hukumar Augie tare da sace dabbobin al’umma.
Kakakin gwamnan Kebbi, Abdullahi Umar Zuru, ya ce Bayan harin ne sojoji suka isa yankin, inda suka ce da wa Allah Ya haɗa su ba da Lakurawan ba.
Sojojin sun kai ɗauki ne bayan roƙon da Gwamna Ahmed Idris ya ce domin kawar da mayaƙan daga jihar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga
- ’Yan bindiga sun lalata tashar wutar lantarkin da ake ginawa a Kogi
Zuru ya ce sojojin sun yi nasarar fatattakar ɓata-garin tare da ƙwato dabbobi da dama da suka tsere suka bari.
Ana iya tuna cewa Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu, ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba sojoji za su fatattaki Lakurawa daga Nijeriya.
Lamarin Lakurawa jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara ya haifar da damuwa da ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan.
Ana zargin masu tsattsuran ra’ayin addinin na iya zama babbar barazanar tsaro fiye da Boko Haram, ganin yadda suke dauke da makamai da ƙwace iko a yankunan karkara tare da aiwatar tsauraran dokokin Musulunci.