Lakurawa: Yadda sojoji ke aikin murkushe ’yan ta’adda

Ministan tsaro ya ce al’ummar yankunan da Lakurawa suka addaba a Jihar Kebbi shaida ne a kan yadda sojoji suka ragargaji mayakan suka fatattake su.

Lakurawa: Yadda sojoji ke aikin murkushe ’yan ta’adda

Ministan Tsaron Najeriya Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. (Hoto: Twitter/@HQNigerianArmy)

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce sojoji suna aiki tukuru don murkushe ayyukan Lakurawa da sauran ’yan ta’adda da ke addabar yankin Arewa.

Ministan wanda ya kai ziyarar aiki tare da duba kayayyakin yakin jirage na rundunar Operation Fansan Yamma, a Jihar Sakkwato ranar Litinin, ya ce sojoji sun dauki wani kwakkwaran mataki kan Lakurawa.

Ya ce, “Kun ji daga bakin shugaban karamar hukumar da Lakurawa suka kai wa hari a Jihar Kebbi, yana bayyana yadda sojoji suka mamaye yankin suka fatattaki Lakurawa

“Hakan ya faru ne sakamakon jajircewa da jami’an tsaronmu suke yi,” a cewar ministan tsaron.

Ya ci gaba da cewa mutanen yankunan da abin ya shafa ne suka fi kowa bakin  da za su yi magana aikin sojoji, domin su ganau ne a kan farmakin da sojoji ke kai wa mayakan.

“Mun kaddamar da wani sabbin makamai a Katsina tare da kaddamar da sabbin jiragen yaki masu saukar ungulu domin ragargazar ’yan fashin daji da  da kuma Lakurawa, kuma za mu sake tura wasunsu zuwa Sakkwato,” in ji ministan.

Ya kai wa sojojin ziyara ne tare da Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Hasan Bala Abubakar da wasu manyan hafsoshin soji.

DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa