Lalacewar ilimi : laifin wane ne?
Masu iya magana na cewa’ilimi gishirin zaman duniya’bugu da kari wani mawaki a cikin wakar sa yana cewa: ‘Duk wanda ba shi da ilimi shi da Jaki mi ke raba su?in ba zancen rashin bindin nam ba! Harkar ilimi a kasar mu ta tabar bare makuta ainun musam man tun daga matakin Firamare da Sakandire […]
Masu iya magana na cewa’ilimi gishirin zaman duniya’bugu da kari wani mawaki a cikin wakar sa yana cewa:
‘Duk wanda ba shi da ilimi
shi da Jaki mi ke raba su?
in ba zancen rashin bindin nam ba!
Harkar ilimi a kasar mu ta tabar bare makuta ainun musam man tun daga matakin Firamare da Sakandire zuwa Jami’a. Shin ko laifin su wanene? Ra’ayi riga! Kowa da irin tasa ni anawa hangen inaga laifin bana wasu kadai bane. Kadan daga cikin wadan da suka taka rawa wajen lalata harkar ilimin su ne kamar haka:- Gwamnati da Malamai da dalibai da kuma Iyaye.
Laifin gwamnati shi ne ta ki inganta rayuwar malamai har su samu ingantaccen albashi da muhalli da sauran abubuwan jin dadin rayuwa.
Domin a wannan karnin albashin mafi yawan malamai baya kai su wani watan rashin muhalli kuma ya sa dimbin malamai suna tsugunne ne a gidajen haya, yau
suna wannan unguwa, gobe suna waccan, inda ake ta har ba su kamar kwallo!
Bugu da kari taki a wadata makarantun da kayan aiki na zamani wadatattu kuma ingantattu. Gine-ginen makarantun sun yi karanci aji daya ya kamata a ce ka da ya wuce dalibai 50 a ciki, amma karancin ajujuwan ya sa ana gwama dalibai fiye da dari daya a cikin dakin karatu daya, sannan ana daukar Malamai ’yan alfarma wadanda ba su cancanta ba saboda suna da Uwa a bakin murhu sai suka zama Malamai. Kadan ke nan daga laifukan gwamnati.
Wasu Malamai suma suna da nasu laifi, kamar kin zuwa aiki cikin lokaci da tashi ba a kan lokaci ba kin bada himma wajen koyar war duk da nasan akwai karancin kayan koyar war to amma yaka mata Malami shima ya ba da tasa gudum muwar wajen koyar war ta fannin iliminsa hikima da kuma dabarar sa domin talla fama yaran su samu ilimin. Haka wasu Malaman sukan rinka lalata da daliban su ta hanyar yaudarar daliban da niyar za su tallafa musu wajen ba su amsa ko cin jarabawar wanda hakan ya sa dalibai da iyaye guje wa makarantar.
Wani malamin yakan wulakantar da dan albashin sa ta hanyar da ba ta dace ba, inda daga bisani ya zauna yana tagumi ya kagara wata ya kare. Wasu dalibai suna da nasu laifi kamar haka. Wasu daliban basa son zuwa makarantar ko da sun baro gida da niyar zuwa Makarantar sai su buge a gidan kallon kwallo ko shagon Tb Game ko dakunan abokanai da kawaye ko dakin samari yayin da wasu kuma sukan je kasuwan cin da baya kashe masu kishir wa yayin da wasu daliban kuma sai su labe a wuraren shaye-shayen miyagun kwayoyi inda suke bura rewa!
Ya yin da wasu daliban ba sa bai wa Malaman nasu cikak ken goyon baya ko yin ladabi da biyayya ga Malaman, walau ko don suna ganin iyayen su sunfi Malaman kudi da jin dadi ko kuma daliban su ga sun girmi Malamai a shekaru ko kuma suna wulakan ta Malaman saka makon juyewar kwakwalwar daliban sanadiyar shan kayan sa maye!
Babban laifin wasu iyaye sukan nuna halin ko oho ga neman ilimin
’ya’yan nasu ta hanyar zura wa ’ya’yaan ido su yi abin da suke so, yayin da
wasu iyayen ke dora wa ’ya’ya tallace-tallace madadin karatun nasu wasu
kuma iyayen hatta biro ko fensir ba sa saya wa yaron nasu, amma za su iya
kashe dubban kudi wurin shagalin biki!
Wannan kuma ba karamar mum munar rawa ba ce al’umma suke takawa wajen ruguza ilimin ’ya’yan.Saboda haka nake bai wa Gwamnati da Malamai da dalibai da Iyaye shawara, kan lallai ya kamata su hada karfi da karfe domin samar wa ’ya’yan su ingantaccen ilimi.
Duba da ganin ’ya’yan su ne za su zamo shugabannin gobe. Kuma idon
har suka bai wa ‘’ya’ya ilimi, to sun sauke nauyin da ke kansu. Za kuma su samu lada daga wurin Ubangiji. Idan suka nuna halin ko oho da ilimin za su gamu da fushin Ubangiji, domin idon ba su bai wa yara ilimin ba, shugabannin gobe za su zamo marasa ilimi, wanda su ma rashin ilimin zai sa ba za su bai wa ilimin muhimmanci ba.
A karshe ina ganin ya kamata a tallafa wa wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari da ke da niyyar inganta ilimin domin ci gaban ’ya’yan mu da mu kan mu da kasar mu baki daya.
Haruna Muhammad Katsina, shi ne, Shugaban kungiyar Muryar Jama’a.Reshen Jihar Katsina. 07039205659 ko 07057491050. [email protected]