Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta
Fasinjoji da dama sun bayyana damuwarsu dangane da jinkirin da aka samu wajen tunkarar lamarin, suna masu alaƙanta hakan da rashin kula da aikin jigilar jirgin ƙasa kyauta.
Ɗaruruwan fasinjoji ne suka maƙale na tsawon kwanaki biyu a tashar jirgin ƙasa ta Warri da ke Jihar Delta, biyo bayan lalacewar jirgin ƙasa da ke jigilar fasinjoji kyauta da aka fara lokacin bukukuwan Kirisimeti.
Lamarin ya haifar da takaici a tsakanin matafiyan.
Shaidun gani da ido sun bayyana lamarin a matsayin abin ruɗani, inda jama’a ke ƙara tururuwa cikin rana.
Fasinjoji da dama sun bayyana damuwarsu dangane da jinkirin da aka samu wajen tunkarar lamarin, suna masu alaƙanta hakan da rashin kula da aikin jigilar jirgin ƙasa kyauta.
“Abin takaici ne cewa mun maƙale a nan kwana biyu,” wani fasinja da ya maƙale ya koka. “Wataƙila saboda jigilar jirgin kyauta ne, ba sa tunanin yana da mahimmanci a kula da shi yadda ya kamata.”
Aikin jigilar jirgin ƙasa na kyauta, wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar, an yi hakan ne domin sauƙaƙa tafiye-tafiye ga ‘yan Najeriya a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Umurnin, wanda ya bai wa ‘yan ƙasar damar yin tafiye-tafiye ba tare da farashi ba daga ranar 20 ga Disamba zuwa 5 ga watan Janairu da farko gwamnati ta yaba da shi a matsayin wani tunani don sauƙaƙawa al’umma.
Sai dai kuma lalacewar jirgin ƙasa a tashar Warri ta jefa shirin cikin wani yanayi, abin da ya sa fasinjojin cikin takaici da maƙalewa.
“Mun yaba da ƙoƙarin gwamnati, amma wannan lalacewar ta jawo mana illa fiye da yadda muke ganin kyanta,” in ji wani fasinja. “Dole ne hukumomi su yi gaggawar gyara jirgin tare da taimaka mana mu ci gaba da tafiya.”
Har ya zuwa lokacin wannan rahoton, ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da musabbabin lalacewar jirgin da kuma lokacin da za a ci gaba da jigilar fasinjojin.