Lalacewar zamantakewa a Arewa ta sa nake wakokin zaman lafiya – Andy Bature

Andy Bature daya ne daga cikin mawakan Hausa da ya yi fice a yankin Arewa maso Gabas. Shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar Mawaka ta Jihar Bauchi kuma shugaban kamfanin waka da daukar bidiyo na Bature Media Consults da ke Bauchi, malamin gonar wanda ya koma mawaki ya bayyana wa wakilinmu dalilin da ya sa yake […]

Lalacewar zamantakewa a Arewa ta sa nake wakokin zaman lafiya – Andy Bature
Lalacewar zamantakewa a Arewa ta sa nake wakokin zaman lafiya – Andy Bature

Andy Bature daya ne daga cikin mawakan Hausa da ya yi fice a yankin Arewa maso Gabas. Shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar Mawaka ta Jihar Bauchi kuma shugaban kamfanin waka da daukar bidiyo na Bature Media Consults da ke Bauchi, malamin gonar wanda ya koma mawaki ya bayyana wa wakilinmu dalilin da ya sa yake wakokin zaman lafiya maimakon na soyayya da suka fi tashe a yanzu:

Mene ne ya ba ka sha’awar shiga harkar waka?
Sunana Andy Bature. Abin da ke burge ni a harkar waka shi ne kasancewarta wata hanyar isar da sako ga dimbin jama’a a lokaci guda kuma ga daukaka da karramawar da ke cikinta. Waka baiwa ce idan kana da baiwa ko da sha’awar ko ba sha’awar baiwar za ta lalubo ka. Na tashi na ga ana waka sai na ji sha’awarta, lokacin da muke yara mun tashi muna wakokin tashe da sauransu a unguwanninmu da yake na taso cikin Hausawa Musulmi duk da kasancewata ba Musulmi ba. Bayan na tafi makarantar sakandare a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Enugu sai ya zamo cewa waka darasi ne na dole. Sai na dauki waka a matsayin darasina na karance ta. Bayan nan sai sha’awar wakar ta zo min.
Shin a can Enugu da Hausa kuke koyon wakar?
Wani abu da ya burge ni a can akwai darusan harsuna uku da ake yi a can, wato Hausa da Ibo da Yarbanci. Idan kan Bahaushe ne, tilas ka dauki Ibo ko Yarbanci, idan Ibo ne tilas ka dauki Hausa ko Yarbanci, idan Bayarbe ne ka dauki Ibo ko Hausa, wato wajibi ne ka koyi yaren da ba naka ba. Koda yake ba da Hausa ake koya mana wakar ba, amma waka wata aba ce da ko da wane yare kake yi kusan yawancin abubuwanta daya ne, yaren ne kawai zai bambanta.
Da ka gama sakandaren a jami’a ka ci gaba da nazarin waka ce?
Da na shiga jami’a farko na fara karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na fara karanta tarihi da kayan tarihi. Daga baya na dawo Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke nan Bauchi inda na karanta aikin gona da tsimi (Agric-economic).
Kana nufin manomi ne ya zama mawaki?
Eh, to noman ma wani lokaci bai yiwuwa sai da waka, z aka manomi yana noma yana waka ana huda ana waka. Wani abu kuma da ya kamata a fahimta za a iya amfani da waka a harkar noma ta hanyar fadakar da manoma. Kamar yanzu a matsayina na malamin gona ina iya yin wakar da ta shafi wani sabon iri da aka samu na masara da yake nuna a wata biyu da sauransu.
Lokacin da kake makaranta ka dauki wani abu na harkar noma ka wake shi?
Na dai rubuta, amma ban fitar a wake a kaset ba.
Kasacewarka malamin gona ka ci gaba da koyarwa ko ba da shawara ko harkar wakar ce ta dauke ka?
Wakar ce ta dauke ni, duk da yake ina taba noma da kiwo na kashin kaina.
Ka kai kamar shekara nawa kana harkar waka?
Na kai akalla shekara 12 ko fiye ina harkar waka, in fito in dauki waka a matsayin sana’a na kai akalla shekara 12 zuwa 15.
Me ya sa ka fi yin wakokin zaman lafiya, ko hakan na da alaka da rikicin addini da kabilanci da yankinka ya yi fama da shi ne?
Na fi mayar da hankali ga wakokin zaman lafiya ne, saboda na yi la’akari da gurbacewar al’umma musamman a bangaren lalacewar zamantakewa a nan Arewa. Na tashi na iske muna cudanya a tsakanin mu mabiya addinai da kabilu cikin mutunci da girmama juna. Ni dan kabilar Zar (Basayi) ne Kirista, amma galibin abokaina Hausawa ne Musulmi, mun rayu cikin girmama juna da mutunta juna. Amma yau abin takaici da bakin ciki muna ta gaba da juna saboda hassada da kyashi da suka shiga zukatanmu. Ganin haka ne ya sa na ga ya kyautu in rika jawo hankalin al’ummarmu ta Arewa ta yi kokarin sarrafa bambance-bambancenta na addini da kabila ta hanyar da za ta ci amfanin hakan, maimakon ruguza kanta. Idan ka je Kudu inda na yi sakandare, in kai dan Arewa ne babu ruwansu da addini ko kabilarka suna daukarka a matsayin Malam Bahaushe ne. To me ya sa mu a Arewa muke bambanta kanmu muke kashe juna da lalata dukiyar juna? Wannan ne dalilin da ya sa nake amfani da ’yar basirar da Allah Ya ba ni don fadakar da mu muhimmancin zaman lafiya da illar tashe-tashen hankula.  
Ko waka ta dauke ke zuwa wasu kasashe da jihohi a nan Najeriya?
Waka ta kai ne kasashen Afirka kamar su Nijar da Chadi da Kamaru da Gabon da Burkina Faso duk harkar waka ta kai ni. A Najeriya, sai dai in kirga jihohin da ban je ba, don su ne kadan, saboda  wadanda na je sun fi wadanda bai je ba yawa, kuma duk harkar waka ce ta kai ni.
Ka taba shiga wata gasa ta waka?
Eh, da jimawa na shiga. Akwai gasar da aka yi a nan Bauchi koda yake ta jima sosai, lokacin da kamfanin sigari ne Benson and Hedges su suka shirya gasar, sai muka shiga gasar da su P-Skaure da sauransu. P-Skaure suka zo na daya, mu muka zo na uku. Kuma da Hausa muka yi wasan ina jin a shekarar 2000 aka yi gasar.
Shin kana da kamfani ne ko kana wakar ce kawai ta neman abinci?
Ina da kamfanoni ba ma kamfani ba, domin ina da kamfanin shirya wakoki zalla wato situdiyo da kuma na daukar faya-fayen bidiyo na shirya labaran tarihi ko dauka da tace fina-finai da ita kanta wakar da ake daukar bidiyonta.
Mutum nawa ke aiki da kamfaninka?
Mutanen da ke karkashina na dindindin mutum goma sha bakwai ne, akwai kuma ma’aikatan wucin- gadi.
Wadanne fitattun mutane ne waka ta hada ka da su?
Waka ta  hada ni da manyan mutane da dama da suka hada da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu. A wakar yabon ayyukan da ya yi ne na fara fice a Jihar Bauchi. Kuma wakar ce ta sake hada ni da Mai girma tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda, wanda duk da yanzu ba ya kujerar Gwamna ya ci gaba da rike ni amana. Sannan akwai Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima, yanzu haka in ka je Borno za ka ji gidajen rediyo da talabijin suna amfani da wakokina na zaman lafiya. Ga tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako, akwai Cif Timawus Mathias da sauransu, Ga Shugaban Ma’aikata na Jihar Bauchi Abdon Dala Gin Kaigaman Dass da sauransu da dama, ga wadda take kamar matsayin uwa gare ni Hajiya Hauwa Biodun Yuguda matar tsohon Gwamna Yuguda . A baya-bayan nan akwai Darakta Janar na Hukumar Tallafin Gaggawa ta Tarayya (FEMA).
Ka taba samun wata lambar yabo a waka?
Na samu lambobin yabo da dama a harkar waka, kalilan daga ciki, na samu lambar yabo daga Majalisar dinkin Duniya da hadin gwiwar wata kungiya a matsayin Jakadan Zaman Lafiya (Peace Ambassador Award) a birnin Maiduguri. Sannan Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ba ni lambar yabo. Sannan gidan talabijin mallakar Jihar Bauchi (BATb) ya ba ni lambar yabo. Cfraz film institute, SUG ATBU, Man’o’War, Zuma Film Festibal, da sauransu duk sun ba ni lambar yabo.
Me ya taba ba ka haushe a harkar waka?
Abin da ya taba ba ni haushi sosai a harkar waka shi ne hana ni wasa da wani dan Kudu ya yi a bikin auren ’ya’yan tsohon Gwamna Yuguda kawai don ya yi min coge ni kuma na nemi hakkina.
Za ka so danka ya gaje ka a waka?
A gaskiya ba na sha’awar in samu magaji a harkar waka a cikin ‘ya’yana. Ba domin sana’ar wakar ba ta da kyau ba, amma do hadarurrukan da ke tare da ita da kuma rashin goyon baya musamman daga gwamnati da jami’o’i da kuma ’yan kasuwa. Idan ka lura, a cikin dukkan mawaka, wadanda suka yi fice ba su wuce kashi goma cikin 100.
Ko akwai wasu mawaka da ka taba koya musu suka zama fitattu?
Babu shakka, akwai mawaka da dama har da ’yan wasan kwaikwoyo kamar su Ibrahim Takondo da Buhari Muhammad wanda ya yi wakar nan ta Gwamnan Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura “Mun yi na farko, mun yi na karshe, Mun yi abin da ba za a kuma ba,” da Ahmad Baba da Motar Kara, da dantandu da Nesho da sauransu. Akwai kuma wadanda muka jima muna tare a harkar kamar su yayana Haruna Aliyu Ningi da Baushe da Umar Yabon Gwani da Bala Busuri da sauransu.