Lalata da Ɗalibai: An tuɓe shugaban tsangayar aikin lauyan Jami’ar Kalaba

Jami’ar Kalaba ta tsige Farfesa Cyril Ndifon daga matsayinsa ta kuma haramta masa shiga harabartakan zargin lalata da ɗalibai

Lalata da Ɗalibai: An tuɓe shugaban tsangayar aikin lauyan Jami’ar Kalaba

Hoton dalibai da suka yi zanga-zanar neman a sallama Farfesa Ndifon a Jami’ar Kalaba.

Jami’ar Kalaba ta cire Shugaban Tsangayar Aikin Lauya, Farfesa Cyril Ndifon daga matsayinsa tare da  dakatar da shi daga aiki, saboda zargin da ɗalibai mata ke masa na yin lalata da su.

Shugabar Jami’ar Farfesa Florence Obi ta kuma haramta wa lakcaran, wanda ya yi ƙaurin suna kan lalata da ɗalibai masu kananan shekaru, daga shiga harabar jami’ar, sai idan kwamitin binciken zargin da ake masa ne ya neme shi.

Karo na biyu ke nan daga shekarar 2015 da zargin lalata da ɗalibai ya sa jami’ar ta dakatar da Cyril Ndifon, wanda shi ne ɗan asalin Jihar Kuros Riba na farko da ya zama farfesa a fannin aikin lauya.

Sanarwar da Rajistaran jami’ar ya fitar ta ce an dakatar da Farfesa Cyril ne saboda zargin sa da saɓa dokokin jami’ar.

Dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar 18 ga Agusta 2023, bayan rashin gamsuwar Shugabar Jami’ar da bayanin Farfesa Cyril Ndifon game da zargin da ɗaliban nasa mata ke masa.

A ’yan kwanakin da suka wuce ne ɗalibai mata daga Tsangayar Aikin Lauya ta jami’ar ɗauke da kwalaye suka yi zanga-zangar neman a sallami Farfesa Ndifon bisa zargin sa da lalata da su.