Lalata dalibi ya kai malamin sakandare kurkuku

Kotu ta tsare wani malamin sakandare a kurkuku kan yin lalata da dalibinsa dan shekara 12.

Lalata dalibi ya kai malamin sakandare kurkuku

Daurin Kotu

Kotu ta tsare wani malamin sakandare a kurkuku kan yin lalata da dalibi dan shekara 12.

Kotun Majistare da ke Ikeja a Jihar Legas ce ta ba umarnin tsare malamin mai shekaru 43 da ake zargi.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Insp John Iberedem, ya shaida wa alkali cewa a rana 18 ga watan Yuni ne wand ake zargin ya yi luwadi da yaron a makarantar sakandaren Katolika ta St Francis Catholic da ke yankin Ikotun.

An gurfanar da malamin ne gaban Mai Shari’a E. Kubeinje, a ranar Litinin.

Alkalin ya ba da umarnin a ci gabaci da tsare wanda ake zargin zuwa lokacin da Ofishin Shari’ar Al’umma (DPP) za na da bahasi kan mataki na gaba. (NAN)