Lallai Jam’iyyar APC ta duba manufar mika ragamar jam’iyyu ga sababbin Gwamnoni

daya daga cikin ka`idojin da aka ce an kafa babbar jam`iyyaradawa ta APC, da ta samu rijista a kusan karshen shekarar da ta gabata, bayan jam`iyyun adawar nan na ANPP da ACN da CPC da DPP da wani bangare na APGA sun amince sun narke sun zama jam`iyyar APC, shi ne jihar da duk wadannan […]

Lallai Jam’iyyar APC ta duba manufar mika ragamar jam’iyyu ga sababbin Gwamnoni
Lallai Jam’iyyar APC ta duba manufar mika ragamar jam’iyyu ga sababbin Gwamnoni

daya daga cikin ka`idojin da aka ce an kafa babbar jam`iyyaradawa ta APC, da ta samu rijista a kusan karshen shekarar da ta gabata, bayan jam`iyyun adawar nan na ANPP da ACN da CPC da DPP da wani bangare na APGA sun amince sun narke sun zama jam`iyyar APC, shi ne jihar da duk wadannan jam`iyyu biyar suke da gwamnati, gwamnan wannan jihar shi zama jagoran jam`iyyar ta APC. Inda kuma babu, to, tsohon gwaman kowani jigo na daya daga cikin wadancan jam`iyyu a jihar shi zai kasance jagoran APC din. Abin tambaya a nan shi ne, ko wadanda suka zauna suka fito da wannan tsari ba su yi hasashen cewa hakan ka iya haifar wa jam`iyyar wasu matsaloli ba, kamar yadda suke kunno kai a yanzu ba, a jam`iyyar ta APC, na shigowar wasu gwamnonin wata jam`iyya da ba a shirya wannan yarjejeniya da ita ba, kamar yadda aka samu a PDP a yau.  
Don haka tun farko tsarin, ya tsarin ya bada dama a jihohi 11,da wadancan jam`iyyu na ANPP da ACN da CPC da APGA da suka taru suka kafa sabuwar APC din, kuma suke da gwamnati, wato a jihohin Legas da Edo da Ogun da Ekiti da Barno da Yobe da Nassarawa da Imo da Zamfara da Osun da Oyo, kai tsaye, gwamnonin jihohinsu suka zama jagororin jam`iyyar ta APC, kamar yadda suke a da a wadancan tsofaffin jam`iyyunsu, sannan kuma inda ake da tsofaffin gwamnonin jihohi ko jiga-jigan hadakar a sauran jihohi 25, suka zauna a zaman jagororin APC a irin wadannan jihohi.
 A yanzu maganar da ake ciki, shigowar gwamnonin nan na jam`iyyar PDP biyar daga cikin bakwai a cikin jam`iyyar APC, da suka dade suna rigima da uwar jam`iyyarsu ta kasa da shi kansa shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan bisa zargin yadda ake tafiyar da jam`iyyar PDP din kanta, ba a yinsa akan tafarkin dimokuradiyya da suka zargi shugabanta na kasa Alhaji Bamanga Tukur da aikatawa da kuma neman lallai, sai Shugaba Jonathan ya cikasa alkawarinsa da ya yi na cewa, ba zai sake neman takarar ya tsaya wa jam`iyyar tasu takarar ba a shekarar 2015, muddin ya yi ta 2011. Abin da suka ce ga shi yanzu kuma ya dage akan lallai sai ya sake tsayawa neman wannan takara. Ya sanya sabuwar jam`iyyar ta APC ta canja wancan matsayi ko sharadi da ta gindaya wa kanta.
Aniyar haka ta bayyana a cikin makon jiya, lokacin da aka ji mai rikon mukamin Sakataren yada labarai na jam`iyyar APC, Alhaji Lai Mohammed yana fada wa manema labarai cewa jam`iyyar ta APC ta bada mukaman jagoranci jam`iyyar ga gwamnonin jam`iyyar PDP da suka shigo APC da shugabancin riko da wasu mambobi biyar ga bangaren gwamnan kamar yadda tsarin jam`iyyar ya tanada. Ma`ana dai an dauki jam`iyyar kacokan an ba gwamnonin biyar, haka kuma za ta kasance ke nan, nan gaba ga dukkan gwamnan PDP da ya yanke shawara ya shigo APC.
A cikin makalata da na gabatar a ranar 13-12-13, bayan na bi sawun irin hamayyar da ke tsakanin Gwamna Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso ma Jihar Kano da tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau, na shawarci sabuwar jam`iyyar APC da ta hakura ta bar jagorancin jam`iyyar ta APC a hannun tsohon Gwamna Malam Shekarau, don ko ba komai,  a yau idan za ka rubuta tarihin kafuwar jam`iyyar APC, dole sai ka sa da sunan Mlam Shekarau kana tarihi zai cika, saboda kasancewar shi ya jagoranci ayarin jam`iyyar ANPP a tattaunar da ta haifar da APC, ba ma wannan ba, tsohon gwamna Malam Shekarau shi yagaji gwamna Kwankwaso a shekarar 2003, ya kuma zauna akan wannan kujera har tsawon shekaru takwas, kuma cikin ikon Allah, Gwamna Kwankwaso ya sake dawowa akan wannan kujera, a zaben 2011, da jam`iyyar PDP, ta dara jam`iyyar ANPP da kuri`u sama  da dubu 40.
Kodayake masu iya magana kan ce “bukatar dara kasawa”,wanda kuma babbar bukatar kowace jam`iyya a ko ina, ita ce ta ci zabe, wanda hakan ta sanya tun farko wadancan jam`iyyun adawa hudu, suka narke suka kafa jam`iyyar APC, amma kuma ina ga a tawa gurguwar fahimtar, ya ci a ce shirin ya yi tanadin da za a duba matsyi da zai karbu ga jama`a ta gwamna dake kankujera da tsohon gwamna kowani jigo, kafin a ce gwamna da ke kan kujera, don kawai ya shigo cikin sabuwar tafiyar, a dauki ragamar jam`iyya  a mika masa. alhali ga wadanda suka sha tsangwama da  kyara da wulakanci iri-iri daga ciki da wajen jam`iyyarsu, akan sun rugumi aniyar a rushe jam`iyyarsu a yi sabuwar APC, kuma suna tare da jama`arsu tun daga tushe.
Bisa ga haka da kuma ina sane da cewa wasu tsofaffin gwamnoni da wasu jiga-jigai sun zama mushen gizaka a cikin harkokin siyasar jihohinsu dama kasa baki daya, kamar yadda wasu gwamnonin masu ci yanzu suka zama, kuma mutanensu na ta addu`o`in Allah Ya canja masu su, don haka nike ganin lallai akwai bukatar jam`iyar ta APC din ta sake nazarin tsarin, muddin dai so take ta kai bantanta a zabubbukan  2015. Idan kuma ta bari son kai da son zuciya, da tunanin a baya wane ya ci mutuncin wane a cikin ana tare, har ta haddasa rabuwa,  yanzu kuma sun sake haduwa cikin tafiya daya, don haka kada a bari su wane da su wane su kai labari, to jam`iyyar APC, ta manta da mafarkin da take na karbar mulkin kasar nan a shekarar 2015.  Allah Ka ba mu ikon zaben shugabannin da za su mulki kasar nan cikin gaskiya da adalci, amin summa amin.