Lallai ne gwamnati ta dakatar da raba wa ’yan fim kudi – John Okafor

A wata tattaunawa da shahararren dan fim John Okafor ya yi da jaridar Punch, ya yi Allah wadai da kungiyar ’Yan Wasan Fim Ta Najeriya saboda ziyarar da suka kai wa Shugaba Jonathan a kwanan nan.dan wasan, wanda aka fi sani da lakanin Mista Ibu, ya bayyana cewa kamata ya yi ’yan kungiyar su kaurace […]

Lallai ne gwamnati ta dakatar da raba wa ’yan fim kudi – John Okafor

A wata tattaunawa da shahararren dan fim John Okafor ya yi da jaridar Punch, ya yi Allah wadai da kungiyar ’Yan Wasan Fim Ta Najeriya saboda ziyarar da suka kai wa Shugaba Jonathan a kwanan nan.
dan wasan, wanda aka fi sani da lakanin Mista Ibu, ya bayyana cewa kamata ya yi ’yan kungiyar su kaurace wa rabar Shugaba Jonathan saboda har yanzu bai fitar da kwakkwarar hanyar taimakon harkarsu ta fim ba.
“Lallai ne gwamnati ta dakatar da ba kungiyar ’yan wasan fim kudi, domin ba mu san hanyar da za mu tafiyar da su ba. Wasu mutane ne kawai ke zuwa ofishin na Shugaban kasa, su amshe kudin su lalatar da su, alhali mu ’yan wasa ba mu amfana da irin wannan tallafi.” Inji dan wasan, wanda a kwanakin baya ya fara fitowa a fim din Hausa mai suna Oga Abuja.
Ya kara da cewa: “Da a ce gwamnati za ta ba mu kayan aiki ko ta ba mu mazauni da sai mu da kanmu mu nemo kudin da za mu zuba jari domin gina katafaren otel da kayan cikinsa, domin ta wannan hanya ma za mu iya bunkasa harkar yawon shakatawa. Kuma ta haka za mu iya maido da Hukumar Tace Fina-finai ta Najeriya a harabarmu, mu zauna tare.”
dan wasan ya yi korafin yadda suke samar wa gwamnati kudi masu yawa ta hanyar fina-finansu, amma a ce ba su da mazauni na fada a gani. “Ta yaya za mu rika biyan Naira dubu 50 ga gwamnati kan kowane fim da ake tace mana, a yayin da muke shirya sama da fina-finai dari a wata, amma a ce ba mu da tsayayyen mazaunin gudanar da sana’armu? Ya kamata a ce gwamnati ta yi amfani da irin wadannan kudade da muke samarwa wajen tallafa wa sana’armu domin ta karfafa.”