Lallana zai koma Southampton

Rahotanni sun nuna dan kwallon Liberpool da ke Ingila, Adam Lallana ya fara shirin komawa kulob dinsa na da wato Southampton a karshen kakar wasa ta bana. Lallana wanda bai dade da dawowa daga doguwar jinya ba, yana buga wa Liberpool kwallo ne a tsakiyar fili.  Sai dai a yanzu ba ya cikin ’yan kwallon […]

Lallana zai koma Southampton
Lallana zai koma Southampton

Rahotanni sun nuna dan kwallon Liberpool da ke Ingila, Adam Lallana ya fara shirin komawa kulob dinsa na da wato Southampton a karshen kakar wasa ta bana.

Lallana wanda bai dade da dawowa daga doguwar jinya ba, yana buga wa Liberpool kwallo ne a tsakiyar fili.  Sai dai a yanzu ba ya cikin ’yan kwallon Liberpool da ke sahun farko al’amarin da ya sa ba ya wasa a kan kari.

Lallana ya taba zama Kyaftin din Southampton kuma yana daga cikin wadanda suka taimaki kulob din hayewa gasar Firimiya ta Ingila a shekarar 2012 daga rukunin ’yan dagaji.