‘Lalle ni dan Boko Haram ne amma ban kashe Janar Shuwa ba’

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama wadansu mutum biyu da take zargin ’yan kungiyar Boko Harama ne kuma take zargin daya daga cikinsu da hannu a kisan gillar da aka yi wa marigayi Janar Mamman Shuwa a kofar gidansa da ke Gwange a Maiduguri a ranar 12 g Nuwamban 2012. Mutanen Ali Mohammed da […]

‘Lalle ni dan Boko Haram ne amma ban kashe Janar Shuwa ba’
‘Lalle ni dan Boko Haram ne amma ban kashe Janar Shuwa ba’

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama wadansu mutum biyu da take zargin ’yan kungiyar Boko Harama ne kuma take zargin daya daga cikinsu da hannu a kisan gillar da aka yi wa marigayi Janar Mamman Shuwa a kofar gidansa da ke Gwange a Maiduguri a ranar 12 g Nuwamban 2012.
Mutanen Ali Mohammed da ake kira Amir mai shekara 25 da Mohammed Sani Nafi’u da ake kira Malam Yaro mai shekara 35, Kwamandan Birged ta Uku da ke Kano Birgediya Janar Hamisu Hassan ne ya gabatar da su manema labarai inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne a Unguwar Hotoro da ke birnin Kano.
Birgediya Janar Hassan ya ce an kama Ali Mohammed ne a ranar 30 ga Afrilu yayin da aka Mohmmad Nafi’u washegari. Ya ce binciken farko ya nuna cewa Mohammed Nafiu ya taimaka wa ’yan bindigar da suka kashe marigayi Janar Mamman Shuwa, inda ya gudu daga Maiduguri jim kadan da kashe na Janar din,
 Birgediya Hamisu ya ce Amir yana yin wa’azi a Baga kuma bayanai sun nuna cewa shi ne ya jagoranci mutannesa na Boko Harma tare da ba su kayan aiki a lokacin da suka yi artabu da
jami’an tsaro kafin a kama shugabansu Muhammad Yusuf a shekarar 2009.
Ya ce sojojin sun kama mota kirar basuwaja mai lambar Jihar Delta, GWK 775PP da wayar hannu da kuma Naira dubu 20 a wurin Amir, sai Naira dubu dari uku a hannun Nafi’u. Ya ce wadanda ake zarfin suna taimakon sojojin wajen binciken da suke gudanarwa.
Sai dai a tattaunawarsa da manema labarai Muhammad Nafi’u ya musanta yana da hannu a kisan Janar din inda ya ce “Ba na musun ni dan Boko Haram ne. Ni almajirin Muhammad Yusuf ne tunda dadewa, sai dai ban hannu a kashe Janar Shuwa. Lokacin da aka kashe Janar Shuwa ina kasuwa ina gudanar da harkokina. Wani abokina ne ma ya gaya min batun mutuwarsa.”
A ranar 6 ga Mayu, 2013 sojoji sun ce sun kama wadansu da ake zargi da kashe Janar Shuwa.