Lalong ka gyara hanyoyin Jos ku mu ki  zabenka – Matasan Jos

Hadakar Kungiyoyin Matasan Garin Jos, ta bai wa Gwamnan Jihar Simon Lalong sharadin ya gyara hanyoyin cikin garin Jos, da aka fara aikinsu kamar yadda ya yi alkawari, ko su ki sake zabensa a zabe mai zuwa. Hadakar kungiyoyin matasan wadda ta kunshi kungiyoyi 19 ta yi wannan kashedin ne lokacin da ta kira gangamin […]

Lalong ka gyara hanyoyin Jos ku mu ki  zabenka – Matasan Jos

Shugaban Haxakar Kungiyoyin matasan Garin Jos, Barista Buhari Ibrahim Shehu lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen aikin gayyar.

Hadakar Kungiyoyin Matasan Garin Jos, ta bai wa Gwamnan Jihar Simon Lalong sharadin ya gyara hanyoyin cikin garin Jos, da aka fara aikinsu kamar yadda ya yi alkawari, ko su ki sake zabensa a zabe mai zuwa. Hadakar kungiyoyin matasan wadda ta kunshi kungiyoyi 19 ta yi wannan kashedin ne lokacin da ta kira gangamin matasan garin Jos, don gudanar da aikin gayya na cike ramukan hanyoyin cikin garin da suka lalace a karshen makon jiya.

Da yake zantawa da ’yan jarida a wajen aikin, Shugaban Hadakar Kungiyoyin, Barista Buhari Ibrahim Shehu ya ce gwamnatin Jihar Filato ta Gwamna Lalong ta dauki hanyoyin da za ta gyara a cikin garin Jos. Kamar hanyar Unguwar Rogo da Unguwar Rimi da hanyar Kasuwar New Market da hanyar Rikkos.  Ya ce an fara aikin gyara hanyoyin tun a shekarar 2016, an tone hanyoyi baki daya an yi ramuka, sai aka bar aikin kusan shekara 3 ke nan.

Barista Buhari Shehu ya ce hanyoyi sun shafi kasuwanni da shaguna, baya ga dubban mutanen da suke amfani da su.Ya ce a lokacin rani kowa yana cin wahala a cikin garin, sakamakon yadda aka lalata hanyoyin, inda kura ke tashi da jar kasa sai dai masu shaguna su rufe. “Yanzu kuma da aka shiga damina hanyoyin sun kara lalacewa ruwa na taruwa a kan hanyoyin.  Don haka muka yi rubutu muka kai ofishin Gwamnan cewa a zo a dauki matakin gyara hanyoyin, domin mutanen Jos suna cikin wani mawuyacin hali, saboda lalacewarsu. Amma wata guda ke nan, har yanzu babu wani bayani da aka yi,” inji shi.

“Don haka muka yanke shawarar mu zo mu yi aikin gayya mu tara kudi mu sayi kasa da duwatsu mu cike ramukan da aka haka  a wadannan hanyoyi, domin mutane su samu sauki. Kuma muna son ’yan jarida su gaya wa Gwamnan, lallai a zo a gyara wadannan hanyoyi. Domin idan aka yi zabe ba a gyara wadannan hanyoyi ba, ya zama  ba za a gyara ba ke nan,” inji shi.

Shugaban matasan ya ce tun da Allah Ya sa da kuri’unsu ne Gwamnan ya ci zabe, sun yanke shawarar idan ba a gyara hanyoyin ba, za su dauki matakin wayar da kan jama’ar Jos cewa Gwamna ya yi musu alkawari, kuma ba ya da niyyar cikawa, don haka su canja, su zabi wanda suke ganin zai yi, wannan aiki.  Ya yi kira ga shugabannin al’ummar Jos musamman malamai su tuna cewa su ne suka tsaya suka ce a zabi Gwamna Simon Lalong a zaben shekarar 2015. Don haka su gaya masa gaskiya cewa ba za a kara zabensa ba, matukar bai cika wannan alkawari da ya yi ba.

A lokacin da aka tuntubi Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Filato, Mista Yakubu Dati kan wannan al’amari, ya ce tuni Gwamna Lalong ya yi taro da ’yan kwangilar da suke aikin wadannan hanyoyi. Kuma da zarar gwamnatin jihar ta samu kudi za ta bai wa ’yan kwangilar, domin su koma su ci gaba da aikin gyara hanyoyin.

Kwamishinan ya ce babu wasu aikin hanyoyi da aka yi watsi da su a jihar. Sai dai an dakatar da aikin wasu hanyoyi ne saboda lokacin damina da ake ciki. Domin babu yadda za a yi a ci gaba da aikin gyaran hanya a lokacin damina.