Lalong ya bude makarantun Filato

Jihar Filato za ta sake bude makarantu daga ranar 30 ga watan Oktoba bayan da suka shafe watanni a rufe sakamakon barkewar annobar COVID-19.  Gwamna Simon Lalong, ta bakin Kakakinsa, Dokta Makut Simon Macham, ya ce matakin na zuwa ne bayan wani taro da ya yi da dukkanin masu ruwa da tsaki na jihar a […]

Lalong ya bude makarantun Filato

Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato

Jihar Filato za ta sake bude makarantu daga ranar 30 ga watan Oktoba bayan da suka shafe watanni a rufe sakamakon barkewar annobar COVID-19. 

Gwamna Simon Lalong, ta bakin Kakakinsa, Dokta Makut Simon Macham, ya ce matakin na zuwa ne bayan wani taro da ya yi da dukkanin masu ruwa da tsaki na jihar a kan daukar matakan hana yaduwar cutar a dukkanin makarantun jihar.

Ya ce an horas da malamai da shugabannin makarantun jihar kan matakan hana yaduwar cutar.

Sanarwar ta ce daliban makarantun firamare ‘yan aji shida za su fara karatu daga ranar 19 zuwa 23 ga watan Oktoba, don shirye-shiryen jarrawar fita.

Tun a watan Maris ne dai aka rufa makarantu a dukkan sassan Najeriya da nufin hana coronavirus yaduwa.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram