Lalong ya kafa kwamitin hukunta masu karkatar da fetur a Filato

Za a kama tare da hukunta duk wanda aka samu yana sayar da fetur sama da farashin gwamnati a Filato.

Lalong ya kafa kwamitin hukunta masu karkatar da fetur a Filato

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya kafa kwamiti na musamman domin magance matsalar karancin fetur a jihar.

Mai magana da yawun Gwamnan, Dokta Makut Macham, ya ce kwamitin zai sanya ido ne kan yadda ake rarraba fetur da kuma farashin da ake sayar da shi a jihar.

“An dora wa kwamitin hakkin kama duk wanda aka kama ya saba ka’ida tare kuma da hukunta shi daidai da doka,” in ji Macham.

Sanarwar hakan ta ce, kwamtin zai tabbatar da ganin ’yan kasuwa na sayar da fetur kan farashin gwamnati da tabbatar da wadatarsa musamman a wannan lokaci na bukukuwa da yawan tafiye-tafiye.

Kazalika, kwamtin zai yi tsayin daka wajen tabbatar da ba a karkatar da fetur din da aka turo wa jihar zuwa wasu wurare.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito kwamitin na kunshe da mambobi da suka hada da rundunar ’yan sandan Najeriya da Hukumar tsaro da DSS da NSCDC da NUPRC da NUPENG da sauransu.

(NAN)