Lalong ya nada Rufus Bature a matsayin Sakataren Gwamnatin Filato

Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya amince da nadin Mista Rufus Bature a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar. Wata sanarwa dauke da sanya hanun Mista Izam Azi da aka raba wa ’yan jarida a garin Jos ce ta bayyana haka. Har ila yau sanarwar ta ce Gwamnan ya amince da nada Mista John Dafa’an a […]

Lalong ya nada Rufus Bature a matsayin Sakataren Gwamnatin Filato
Lalong ya nada Rufus Bature a matsayin Sakataren Gwamnatin Filato

Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya amince da nadin Mista Rufus Bature a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar. Wata sanarwa dauke da sanya hanun Mista Izam Azi da aka raba wa ’yan jarida a garin Jos ce ta bayyana haka.

Har ila yau sanarwar ta ce Gwamnan ya amince da nada Mista John Dafa’an a matsayin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin tare da Barista Yusuf Gambo Hawaja a matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar.
Sanarwar ta ce Gwamnan ya amince da nada Mista Cyril Tseyin a matsayin Akanta Janar na Jihar sai Farfesa John Wade a matsayin Daraktan Binciken Kudi da Mista Emmanuel Nanle a matsayin Daraktan Watsa Labarai na Gwamnan.
Gwamna Lalong dai ya yi alkawarin hada kan al’ummar jihar a lokacin mulkinsa. Gwamna Lalong ya yi wannan alkawarin ne a lokacin yake jawabi, bayan an rantsar da shi a matsayin sabon Gwamnan Jihar Filato a babban filin wasa na Rwang Pam da ke garin Jos. Ya ce gwamnatinsa za ta yi haka ne ta hanyar tafiya da dukkan al’ummar jihar tare da zaman tattaunawa da al’umomin da ba sa ga maciji da juna a jihar.
Ya ce “Za mu iyakar kokarinmu wajen ganin an samu tabataccen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar nan, domin babu wani ci gaba da za a samu, idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Har ila yau ya yi alkawarin inganta rayuwar al’ummar jihar ta hanyar inganta hanyoyin tattalin arzikin jama’a da suka hada da noma da kirkiro tsare-tsaren samar da ayyukan yi da bunkasa harkokin kasuwanci, inda ya ce gwamnatinsa za ta sake gina babbar kasuwar Jos da ta kone shekaru da dama da suka gabata.
Sabon Gwamnan ya ce gwamnatinsa na bukatar hadin kan jama’ar jihar wajen magance matsalolin da suke damun jihar ciki.