Lalong ya yi marabus daga Minista ya koma Sanata 

Tsohon gwamnan ya ce ya yi nazari kan yin murabus daga matsayin minista don ciyar da al’ummarsa gaba.

Lalong ya yi marabus daga Minista ya koma Sanata 

Tsohon Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya yi murabus daga kujerar ministan kwadago da samar da ayyukan yi.

Lalong ya ce a hukumance ya mika takardar murabus dinsa ga shugaba Bola Tinubu don ba shi damar zama Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta Kudu.

A cikin wata wasika da ya gabatar wa shugaban kasa a ranar Talata, Lalong ya tunatar da shugaban cewa kotun daukaka kara ta bayyana shi a matsayin zababben Sanatan Filato ta Kudu kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta ba shi takardar shaidar cin zabe.

Lalong ya ce sai da ya yi nazari kafin yin murabus din saboda amana da amincewa da shugaban kasa ya dora masa a matsayin minista a majalisar ministocinsa bayan ya yi aiki a matsayin Darakta Janar na yakin neman zabensa na 2023.

Ya ce, “Duk da haka, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga mazabata, na yanke shawarar zama Sanata don ci gaba da ba da gudunmawa ga yankin da kuma shimfida aiki a karkashin dimokuradiyya”.

An harbe ’yan sanda biyu a Yobe

Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su

Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’