Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al’umma 01
Daga wannan za mu fahimci cewa addinin Musulunci yana ba ran dan Adam kariya fiye da kowane addini ko tsarin rayuwa na dan Adam.Kuma babbar mai tsare rayuka a kowane lokaci ita ce hukuma ko gwamnati. Idan ta ce ita ballagaza ce babu ruwanta da tsare addinin mutane, ko kowa ya je ya yi addinin […]
Daga wannan za mu fahimci cewa addinin Musulunci yana ba ran dan Adam kariya fiye da kowane addini ko tsarin rayuwa na dan Adam.
Kuma babbar mai tsare rayuka a kowane lokaci ita ce hukuma ko gwamnati. Idan ta ce ita ballagaza ce babu ruwanta da tsare addinin mutane, ko kowa ya je ya yi addinin da yake so, ko ya ma ki bin addinin gaba daya, to komai ballagazancinta ba za ta ce, alhakin tsare rayuka ya fadi daga kanta, kowa ya je ya kashe wanda yake so ba. Duk duniya babu inda aka taba samun haka. Don haka muna nasiha ga Musulmin da ke cikin wannan gwamnati, ya alla a bangaren mulki ne ko tsaro, su sani zubar da jinin jama’a da ake yi a kasar nan alhakin yana wuyansu ne su da sauran shugabannin gwamnatin da ba Musulmi ba. Kada su dauka Shugaban kasa ne kawai alhakin ke wuyansa, su ma suna da kaso, abin da zai hana su samun zunubi shi ne idan suka bayar da shawarar yadda za a magance wannan zubar da jini, amma suka lura an ki daukar shawarar saboda dalili na siyasa ko wata manufa, sai su yi murabus daga gwamnatin. Wallahi, ba uzuri ba ne da za su tunkari Allah da shi gobe kiyama cewa ba su ne shugabanni na kololuwa ba, shi ya sa suka kasa yin komai.
Alkur’ani ya nuna mana cewa ko da muguwar magana ko ta banza ko wadda za ta cutar ake yi, idan mutum bai iya hanawa, ya tashi daga wurin. To ina ga zubar da jinin bayin Allah da ake yi, amma hukuma tana rikon sakainar kashi da lamarin? Idan sojojinmu za su ja kasashen waje kwantar da yaki su samu nasara, me zai hana su iya kwantar da yakin da ke gudana a jihohi biyu na kasar nan?
Kwanaki wani soja ya fito a gidan rediyon Muryar Amurka yana kukan cewa akwai lauje cikin nadi dangane da yaki da masu daukar makami a yankin Arewa maso Gabas, amma maimakon mu ji hukumomin tsaro sun dauki matakin bincikar zargin, sai suka ce, wai soja mai da’a ba zai yi haka ba. Sojan nan ya jero zarge-zarge kan kwamandan sojojin Bama, amma ba wani abu daga bangaren gwamnati na a binciki zargin nan. Kuma ga shi kullum kashe mutane ake yi a yankin fiye da kowane yanki.
Ran mumini daya yana da tsada a wurin Ubangiji, shi ya sa a wasu Hadisai Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Wallahi, gushewar duniya ya fi sauki a wurin Allah da kashe mumini ba tare da hakki ba.” A wani Hadisin kuma ya ce: “Rusa dakin Ka’aba ya fi sauki a wurin Allah da kashe mumini ba tare da hakki ba.”
Na uku: Kyautata tsare hankali:
1. An sanya hankali sharadi na takalifanci:
Al-Amadiy ya ce: “Ma’abuta hankali sun hadu kan cewa daga cikin sharadin takalifanci (dora wa mutum hukunci) ya kasance mai hankali. Kuma shi ne mafi muhimmanci ga takalifanci, domin takalifi magana ce, kuma magana da wanda ba ya da hankali kuma ba ya fahimta abu ne korarre, kamar yin magana da dutse ko dabbobi, domin asalin maganar da ake nufi shi ne umarni da hani da suke iya jawo samun lada ko ukuba. Wanda yake umarnin shi ne Allah Madaukaki kuma shi ne ya wajabta da’a, kuma kasancewar wanda ake umarni da yin kaza da kaza kamar mahaukaci da yaron da bai mallaki hankali ba, ana kallonsa kamar dutse ne ko itace da dabba… don haka ake yi masa uzuri kan takalifanci.” (Al-Ihkamul fi Usulil Ahkam, mujalladi na 1 shafi na 138-139).
Saboda haka idan hankali sharadi ne na yin takalifanci a shari’ar Musulunci, to kiyaye shi lalura ne da ba makawa, kuma rayuwar mutane ba za ta daidaitu ba ba tare da shi ba.” (Makasidus Shari’a wa Alakatiha bi Adillatis Shari’a, shafi na 112).
2. Haramta abin da zai bata hankali:
Daga cikin abin da yake nuna kular shari’ar Musulunci wajen tsare hankali akwai cewa ta haramta duk wani abin da zai iya batawa ko gusar da hankali da jawo masa matsala. Kuma wadannan abubuwa masu bata hankali sun kashi gida biyu:
a. Masu bata hankali na zahiri:
Su ne wadanda suke jawo matsala ga hankali ta yadda mutum zai wayi gari kamar mahakuaci, wanda ba zai iya gane masoyi daga makiyi ba, ba zai iya bambance alheri da sharri ba, ya zamo maganganunsa ba su da kan gado, yana mai watsa sirrinsa da ya kamata ya boye. Wadannan masu bata hankali sun hada da giya da kwaya da hodar Iblis da sauran kayayyakin gusar da hankali:
“Ya ku wadanda suka yi imani! Abin sani kawai, giya da caca da refu da kiban kuri’a, kazanta ne daga cikin aikin Shaidan, sai ku nisance shi, wa la’alla ku ci nasara. Abin sani kawai, Shaidan yana nufin aukar da adawa da keta a tsakaninku a cikin giya da caca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga Sallah. To shin ku masu hanuwa ne?” (k:5:90-91).
Sayyid kutub ya ce: “Lallai maye da kowane irin abin maye yana kore fadaka a da’iman da Musulunci ya farlanta a kan zuciyar Musulmi domin ya kasance sadarwa a tsakaninsa da Allah ba ta yankewa a kowace lahaza tana mai kiyaye dokokin Allah a kowane motsi. Kuma sa’annan ya kasance da wannan fadaka yana mai aiki na wajibci domin inganta rayuwa da kyautata tad a kare ta daga yin rauni ko fasadi, ya yi amfani da aiki da ita wajen kare ransa da dukiyarsa da mutuncinsa da tsare zaman lafiyar jama’ar Musulmi da shari’arta da dokokin zamantakewarta daga dukkan wata ta’adda. Musulmi a tilonsa ba a bar shi ga dabarar kansa ko jin dadin kansa ba, a kansa akwai takalifofi da suke wajabta masa kasancewa a fadake, akwai takalifofi na Ubangijinsa akwai takalifofi na kashin kansa, akwai takalifofi na iyalansa, akwai takalifofi na jama’ar Musulmin da yake raye a cikinta da kuma takalifofi na Musulunci dukkansu na yin kira zuwa gare su da bayar da su. Ana bukatar ya kasance a fadake koyaushe domin ya sauke wadannan takalifofi. Kai hatta a lokacin da yake jin dadi da abubuwa tsarkaka, Musulunci ya bukaci ya kasance a fadake a cikin wannan jin dadi, domin kada ya zamo bawa ga sha’awoyinsa ko wannan dadi. Ya zamo da’iman ya fi karfin kwadayinsa ya tankwara shi ya zamo mai bin umarninsa ba shi ya zamo mai bi ga kwadayinsa ba. To idan maye ya kama mutum ba zai iya kiyaye komai daga cikin wadannan abubuwa ba.” (Fi Zilalil kur’an, mujalladi na 2, shafi na 977).
Ya ci gaba da cewa: “Sa’annan wannan bacewar hankali a hakikaninta ba komai ba ce face guduwa daga hakikanin rayuwa a wani lokaci daga cikin lokuta da rusuna ga wasu surori da suke mamaye tunanin mutum. Kuma Musulunci yana kin wannan hanya ga Musulmi. Yana nufin mutane su rika ganin hakikanin al’amura su fuskance su yadda ya kamata, su rayu a cikin duniya suna masu gudanar da rayuwarsu gwargwadon yadda ya kamata, kuma irin wannan rayuwa ba za ta samu a bisa wahami da rudu ba… Kuma fuskantar hakikanin al’amura ita ce ginshiki mai girma da karfin ikon gudanar da rayuwa. Amma guje mata zuwa ga wahamomi wata hanya ce ta aukawa ga rudu da rauni da ruguzawa. A cikin kyawun Musulunci da’iman yana sanya tarbiyyar manufa a gaba da kubutar da ita daga daurin al’adu masu tilasta karkacewa da gushewar hankali, wannan buguwa da gushewar hankali ana daukarsa shi kadai a matsayin wani aikin Shaidan da ke iya lalata rayuwar mutum.” (Fi Zilalil kur’an, mujalladi na 2, shafi na 977).