Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al’umma (1)
Lalurori biyar:Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya sanya shugabanci ya zama hanyar tsare rayuwa da dukiya da hankali da addini da nasaba. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya nuna cewa Shugaba zai tashi Ranar kiyama daddaure da sarka, in ma adalcinsa ya kwance shi, ko kuma zaluncinsa […]
Lalurori biyar:
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya sanya shugabanci ya zama hanyar tsare rayuwa da dukiya da hankali da addini da nasaba. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya nuna cewa Shugaba zai tashi Ranar kiyama daddaure da sarka, in ma adalcinsa ya kwance shi, ko kuma zaluncinsa ya tunkuda shi cikin wuta.
Bayan haka, daga yau za mu fara duba wasu abubuwa biyar ne da shari’a ta dora wa shugabanni alhakin tsare su ga wadanda suke mulka. A nan muna nufin shugabannin da mulki na hakika ke hannunsu ne kamar gwamnoni da Shugaban kasa a yayi irin na Najreriya.
Imam As-Shadabi ya ce: “Takalifofin shari’a (wato abin da shari’a ta farlanta) suna juyawa ne kan tsare manufofinta a cikin halitta, kuma wadannan manufofi ba su wuce uku ba:
1. Su kasance lalurai.
2. Su kasance bukatu.
3. Su kasance kyautatawa.
Amma lalurai, ma’anarsu su kasance ba makawa daga gare su su tsayu wajen gyaran addini da duniya ta yadda idan aka rasa su gyaran duniya ma ba zai yiwu ba, maimakon haka sai fasadi da ashin hankali da asarar rauwa su auku. A Lahira kuma a rasa tsira a rasa ni’ima a tashi da asara mabayyani… Lalurori biyar sun kushi: Kiyaye addini da raid a nasaba da dukia da kuma hankali.” (3)
Algazali kuwa cewa ya yi: “Makasudin shari’a game da halitta guda biyar ne: Su ne ta kiyaye musu addininsu da rayukansu da hankalinsu da nasabarsu da dukiyarsu. Duk abin da ya kunshi kiyaye wadannan ginshikai biyar, to shi maslaha ne, duk kuma abin da ya gaza samar da wadannan ginshikai biyar to fasadi ne, kuma kawar da shi maslaha ne. Kuma wadannan ginshikai biyar kiyaye su yana cikin tartibin lalurori, kuma su ne mafi karfin martaba a cikin maslahohi.” (4).
1. Dalilai kan kiyaye lalurori biyar:
a. Daga cikin Alkur’ani:
Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce: “Ku zo in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta.” Wajibi ne a kanku kada ku yi shirkin komai da Shi, kuma game ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatawa, kuma kada ku kashe ’ya’yanku saboda talauci, Mu ne Muke azurta ku, ku da su, kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha, abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, face da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi: tsammaninku, kuna hankalta. Kada ku kusanci dukiyar maraya face da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga karfinsa. Kuma ku cika mudu da sikeli da adalci, ba Mu kallafa wa rai face iyawarsa. Kuma idan kun fadi magana, to, ku yi adalci, kuma koda ya kasance ma’abucin zumunta ne.” (k:6:151-152).
A cikin wadannan ayoyi suna bayyana kula da tsare wadannan lalurori bayyanawa ta zahiri a fili.
Hakiki ya zo game da kiyaye addini ta hana yi wa Allah Madaukaki shirki, kuma sai kiyaye rai ya zo a cikin fadinSa: “Kada ku kashe ’ya’yanku saboda talauci.” (k:6:151) da kuma fadinSa “Kada ku kashe rai wadda Allah Ya haramta, face da hakki.” (k:6:151). Sai kuma kiyaye nasaba cikin fadinSa” Madaukaki: “Kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu.” (k:6:151). Daga cikin manyan abubuwan alfasha akwai zina wadda Allah Madaukaki Ya siffanta da alfasha a cikin fadinSa: “Kuma kada ku kusanci zina, lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya.” (k:17:32). Kuma ya zo game da kiyaye dukiya cikin fadinSa Madaukaki: “Kada ku kusanci dukiyar maraya face da siffa wadda take ita ce mafi kyau.” (k:6:151) da kuma fadinSa: “Ku cika mudu da sikeli da adalci.” (k:6:151).
Kiyaye hankali kuma ana daukarsa ne daga kunshin takalifai na kiyaye sauran lalurori. Domin wanda ya bata hankalinsa ko ya rasa hankali ba zai iya aikin tsare wadannan lalurori kamar yadda Allah Ya yi umarni ba. La’alla saboda nuni kan haka ne a karshen aya ta 151 Allah Ya ce: “Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi: tsammaninku, kuna hankalta.” (k:6:151). (5)
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kowa face Shi, kuma game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai dayansu ya kai ga tsufa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu ‘tir’ kuma kada ka tsawace su, kuma ka fada musu magana mai karimci. Kuma ka sassauta musu fikafikan tausasawa na rahama. Kuma ka ce: “Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi renona, ina karami. Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rayukanku. Idan kun kasance salihai, to, lallai ne Shi Ya kasance ga masu komawa gare Shi, Mai gafara. Kuma ka bai wa ma’abucin zumunta hakkinsa da miskini da dan hanya. Kuma kada ka bazzara dukiyarka, bazzarawa. Lallai mubazzarai sun kasance ’yan uwan Shaidanu. Kuma Shaidan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kafirci. Ko dai ka kau da kai daga gare su domin neman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fatanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi. Kuma kada ka sanya hannunka kukuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfida shi dukan shimfidawa, har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa. Lallai ne Ubangijinka Yana shimfida arziki ga wanda Yake so, kuma Yana kuntatawa. Lallai Shi Ya kasance Masani ga bayinSa, Mai gani. Kuma kada ku kashe ’ya’yanku domin tsoron talauci. Mu ne ke azurta su, su da ku. Lallai ne kashe su ya kasance kuskure babba. Kuma kada ku kusanci zina. Lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya. Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki, kuma wanda aka kashe, yana wanda aka zalunta, to hakika, Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ketare haddi a cikin kashewar. Lallai shi ya kasance wanda ake taimako. Kuma kada ku kusance dukiyar maraya face dai da siffa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi karfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lallai alkawari ya kasance abin tambayawa ne. Kuma ku cika mudu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikeli madaidaici. Wancan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara. Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi. Lallai ne ji da gani da zuciya, dukan wadancan (mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya. Kuma kada ka yi tafiya a cikin kasa da alfahari. Lallai kai, ba za ka huda kasa ba, kuma ba za ka kai ga duwatsu ba ga tsawo. Dukan wancan, mai muninsa ya kasance abin kyama a wurin Ubangijinka.” (k:17:23-38).