Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al’umma (3)
Kyautata tsare addini: 1. Aiki da addini:Allah Ya wajabta haddi mafi karanci na tsare wannan addini a kan kowane daya daga cikin al’ummar Musulmi. Shi farali ne na aini da bai faduwa daga kan kowa matukar yana da ikon tsayar da shi, iko na hankali da iko na aiki, kuma hakan misalin tushe ne na […]
Kyautata tsare addini:
1. Aiki da addini:
Allah Ya wajabta haddi mafi karanci na tsare wannan addini a kan kowane daya daga cikin al’ummar Musulmi. Shi farali ne na aini da bai faduwa daga kan kowa matukar yana da ikon tsayar da shi, iko na hankali da iko na aiki, kuma hakan misalin tushe ne na Musulunci da imani. (Al-Islam Wad Daruratil Hayat, shafi na 31).
Sheikhul Islam ya ce: “Hakika Annabi (SAW) ya ambaci addini da cewa shi ne mika wuyan bawa ga mahaliccinsa mikawa mudalaki, wanda yake wajabta ibada ga Allah wajabta ta yanke a kan kowane mutum. Don haka ya wajaba a kan duk wanda yake da ikon ya bauta wa Allah da su yana mai tsarkake addini gare Shi, wadannan su ne biyar din, duk abin da ke koma bayansu to yana wajaba ne ta sabuba na gyara, wajibcinsa ba zai game daukacin mutane ba.” (Majmu Alfatawi, mujalladi na 7, shafi na 314).
Kuma akwai haddi mafi karanci na abubuwan da aka haramta, Allah Ya yi gargadi kansu a kan kowane mutum, su ne muharramai na aini da ake neman kowane mutum ya guje musu. Su ne muharramai da aka tsoratar kan zatinsu saboda abin da ke shafar mutum shi kadai ko jama’a na cutarwa sakamakon aikata su, kamar zina da shan giya da kashe rai wadda Allah Ya haramta ba tare da hakki ba da sauransu. Sannan akwai abin da ya haramta ga kowane mutum daga cikin al’umma, face abin da ya zama an tilasta shi zuwa gare shi, na daga cikin abin da ba zai rayu ba, sai tare da shi na abin da zai iya amfani da shi kamar cin mushe. Hakika Allah Ya hukunta sa’adar duniya da babban rabo a Lahira ne a kan kwatanta umarninSa da guje wa haninSa, kamar yadda Ya hukunta tabewa a duniya da Lahira a kan wanda ya saba masa kamar yadda Madaukakin Sarki Ya ce: “Ina rantsuwa da zamani. Lallai ne mutum yana a cikin hasara. Face wadanda suka imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri (su kam, ba su cikin hasara).” (k:103:1-3).
Ibnu Kasir ya ce: “Sai (Allah) Ya yi istisna’in imani daga yin hasarar wadanda suka yi imani da zukatansu kuma suka yi ayyukan kwarai da gababunsu “Kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya” wadda ita ce maganin yin da’a da barin muharramai.” (Tafsir Alkur’anil Azim, mujalladi na 4, shafi na 58).
2. Hukunci da addini:
Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne Mu, Mun saukar zuwa gare ka, Littafi da gaskiya, domin ka yi hukunci a tsakanin mutane da abin da Allah Ya nuna maka…” (k:4:105).
Ibnu Sa’adi ya ce: “Hukunci a nan ya shafi hukunci a tsakaninsu cikin jinane da mutunci da dukiya da sauran hakkoki da a cikin akidoji da daukacin mas’alolin hukunce-hukunce.” (Tafsirul Karimur Rahaman, shafi na 199).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar.”
Ibnu Kasir ya ce: “Ma’ana ka yi hukunci -ya Muhammad- a tsakanin mutane, Larabawansu da Ajamawansu, Umiyyansu da Ma’abota Littafinsu da abin da Allah Ya saukar zuwa gare kai a cikin wannan Littafi Mai girma.” (Tafsir Alkur’anil Azim, mujalladi na 2, shafi na 105).
Sheikh Abdullahi kadiri ya ce: “Abin nufi da tsare wannan addini, shi ne a aikata manufofinsa a bayan kasa, ya zamo yana hukunci cikin tasarrufin dan Adam, ya biya hakki ma’abucin hakki, a ba mara gaskiya rashin gaskiyarsa. Domin lallai ne mutane suna ta’addanci sashinsu ga sashi a cikin wadannan lalurori da rayuwa ba ta yiwuwa sai da su. Suna ta’adda a kan addininsu da nasabarsu da mutuncinsu da hankalinsu da rayukansu. Kuma babu wani tsari a tsakanin tsarurrukan da ke bayan kasa da zai iya tsare wadannan lalurori tsarewar da zai kare musu rayuwa ta zamo mai dadi da sa’ada face wannan addini. Don haka hukunci da abin da Allah Ya saukar lalura ce daga cikin lalurorin tsare addini.” (Al-Islam Wad Daruratil Hayat, shafi na 40).
3. Da’awa zuwa ga addinin:
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wane ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na kwarai, kuma ya ce, “Lallai ni, ina daga masu sallamawar al’amari zuwa ga Allah (Musulmi)?” (k:41:33).
Ibnu Jarir ya ce: “Ma’ana; wane ne ya fi kyau ga magana – ya ku mutane- daga wanda ya ce: “Ubangijinmu Allah, sannan ya daidaita ya tsaya a kan imani da Shi, ya tuke ga bin umarninSa da haninSa, kuma ya kira bayin Allah zuwa ga abin da ya ce kuma ya yi aiki da shi daga wannan?” (Jami’ul Bayan, mujalladi na 11, shafi na 109).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wata jama’a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umarni da alheri, kuma suna hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan, su ne masu cin nasara.” (k:3:104).
Ibnu Kasir ya ce: “Allah Madaukaki Yana cewa: “Wata jama’a daga cikinku ta kasance mai tsayuwa ga al’amarin Allah wajen da’awa (kira) zuwa ga alheri da umarni da alheri da hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara.” (Tafsir Alkur’anil Azim, mujalladi na 1, shafi na 398).
Shaihul Islam ya ce: “Lallai gyaruwar bayi tana cikin umarni da alheri da hana abin da ake ki. Kuma lallai ingantar jin dadin rayuwa da su kansu bayi suna cikin yi wa Allah da ManzonSa da’a. Kuma ba za a cimma haka ba, sai da umarni da alheri da hana abin da ake ki, da wannan ne wannan al’umma ta zamo mafi alherin al’umma da aka fitar a tsakanin mutane. Allah Madaukaki Ya ce: “Kun kasance mafi alherin al’umma wadda aka fitar ga mutane, kuna umarni da alheri, kuma kuna hani daga abin da ake ki.” (k:3:110.). Kuma Ya ce: “Kuma wata jama’a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umarni da alheri, kuma suna hani daga abin da ake ki.” (k:3:104). Kuma Madaukaki Ya ce: “Kuma muminai maza da muminai mata, sashinsu majibinta sashi ne, suna umarni da alheri, kuma suna hani daga abin da ba a so.” (k:9:71). Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “To a lokacin da suka manta da abin da aka tunatar da su da shi, Mun tserar da wadanda suke hani daga cuta, Muka kama wadanda suka yi zalunci da azaba mai tsanani domin abin da suka kasance suna yin a fasikanci.” (k:7:165). Sai Allah Ya ba da labari cewa lokacin da azaba ta sauka wadanda suka hana cuta sun tsira, aka kama wadanda suka yi zalunci da azaba mai tsanani.” (Majmu Alfatawi, mujalladi na 28, shafi na 306-307).