Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al’umma (4)
4. Jihadi a tafarkin Allah: Daga cikin hanyoyin kyautatawa da tsare addini akwai jihadi, sai dai mutane da yawa, ciki har da Musulmi, suna gurguwar fahimta ga kalmar jihadi. Sukan dauka daukar makami a yaki mushirikai da kafirai shi ne jihadi, alhali ba haka ba ne. Jihadi yana nufin yin hobbasa domin yada addinin Allah […]
4. Jihadi a tafarkin Allah:
Daga cikin hanyoyin kyautatawa da tsare addini akwai jihadi, sai dai mutane da yawa, ciki har da Musulmi, suna gurguwar fahimta ga kalmar jihadi. Sukan dauka daukar makami a yaki mushirikai da kafirai shi ne jihadi, alhali ba haka ba ne. Jihadi yana nufin yin hobbasa domin yada addinin Allah ta duk hanyar da ta sauwaka, tare da kange hanyoyin da makiya Musulunci za su iya bi wajen dakile kafar isar addinin ga wasu jama’a. Da wannan ne mukatala (yaki) ke iya shigowa karkashin jihadi, mukatala kuwa shi ne mataki na karshe na jihadi, wato ka yi jihadin kiran mutane zuwa ga addini ta hanyar kira da wa’azi, sannan idan aka takura maka ka yi hijira zuwa inda ba za a takura maka ba, sannan idan Musulmi suna da daula, sannan wanda ba Musulmi ba ya yi kokarin yakar ta su ma su dauki makami don yakarsa. Kuma wannan ba zai yiwu a zama irin na kara zube ba, dole sai akwai shugabanci irin wanda shi addinin ya tsara, shugabancin da al’ummar Musulmi suke yi wa biyayya, dau’an wa karhan, domin Allah. Ga duk wanda ya nazarci tarihin Musulunci zai ga cewa, jihadin Musulunci ba jihadi ne na tilasta wa daidaikun mutane su zama Musulmi ba, a’a, jihdai ne na kare daula da akida. Ga daidaikun mutane kuwa “Babu tilastawa a cikin addini.” Idan har aka tilasta wa wani shiga Musulunci, yana iya zama munafuki, ya rika cutar da addinin fiye da wanda ba Musulmi ba.
Don haka bai kamata kawai wani mutum, don ya ci abinci ya koshi, ya ce ku dauki makami ku auka wa wasu jama’a da sunan jihadi ba. Wannan ba jihadi ne na Musulunci ba, sai dai a ce tayar da tarzoma da jawo tashin hankali.
Kuma makasudin yin hijira kafin jihadi shi ne domin zama a cikin gari guda da wadanda za a yaka na iya jefa rayuwar masu jihadin da wadanda suke yaka a cikin hadarin zubar da jini marar alfanu da kashe fararen hular da ba su dauke da makami da halaka mata da yara da tsofaffi da sauransu, wanda hakan ya saba wa koyarwar Musulunci. Masu jihadi kan hadu ne a wani bigire su fafata, idan daya ya samu nasara ya karasa garin wanda ya yi nasara a kansa, yana mai shelar garin ko kasar ta zama tasa, don haka kowa ya yi kaza ya bar kaza, ba shiga garin ake yi a kama sauran mazaunansa da kisa ba. Babu inda aka samu haka a tarihin Musulunci.
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku yake su har wata fitina ba za ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To idan sun hanu, to lallai ne Allah ga abin da suke aikatawa Mai gani ne.” (k:8:39).
Wannan aya tana daga cikin ayoyin da masu da’awar jihadi ke fakewa da ita su rika ganin akwai kafar tilasta wa kowane mutum shiga Musulunci. Sai dai abin tambaya wane malami ne daga cikin magabata ya yi irin wannan fassara ga ayar.
Bari mu saurari yadda Ibnu Jarir ya fassara ayar: “Allah Madaukaki Yana cewa a matsayin tunatarwa ga Annabinsa Muhammad (SAW): “Ku yaki mushirikai wadanda suke yakarku, har ya kasanec babu wata fitina. Yana nufin babu shirka ga Allah, kuma ya zamo ba a bauta wa wani face Shi, a raunana bautar gumaka da ubanningiji da abokan tarayya. Ta zamo ibada da da’a ga Allah Shi kadai banda waninSa na daga gumaka.” (Jami’ul Bayan, mujalladi na 2, shafi na 109).
A fassarar Ibnu Jarir ya ce: “Ku yaki mushirikan da suke yakarku….” Bai ce a auka wa kowadanne mushirikai da yaki ba, to ina ga wanda yake fada wa Musulmi da yaki, ko yake fada wa wanda ba Musulmi ba da bai dauke da makami da yaki?
Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa: “Kuma ba domin tunkuderwar Allah ga mutane ba, sashinsu ga sashi, hakika da an rusa sauma’o’in (Ruhbanawa) da majami’un Nasara da gidajen ibadar Yahudu da masallatai wadanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa.” (k:22:40).
Tirkashi wane addini ne ya kwatanta haka, ya soki rusa wuraren bauta na Yahudu da Nasara da masallatai?
Ibnu Sa’adiy ya ce kan wannan aya: “Wannan yana nuni kan hikimar jihadi, domin lallai makasudinsa shi ne tsayar da addinin Allah, ko tunkude kafiran da suke cutar da muminai, wadanda suke fara far musu da ta’addanci da zaluntarsu, da kuma samun damar bauta wa Allah da tsayar da shari’o’insa mai tsarki.” (Taisiril Karimur Rahaman, shafi na 489).
Kuma Allah Ya sake cewa: “Hakika, lallai Mun aiko ManzanninMu da hujjoji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littafi da sikeli tare da su domin mutane su tsayu da adalci, kuma Mun saukar da bakin karfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfani ga mutane, kuma domin Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lallai ne Allah Mai karfi ne, Mabuwayi.” (k:57:25).
Nan ma Musulunci ya nuna manufar aiko Manzanni ita ce tsayar da adalci a tsakanin mutane, shi ya sa aka aiko su da littafi da mizani. Sannan Allah Ya hore mana bakin karfe ne domin yin makamai da sauran kayayyakin rayuwa, kuma saboda Ya san halayenmu na mutane, sai Ya ce a cikin bakin karfen akwai cutarwa mai tsanani, saboda wasunmu za su rika halaka mutane da shi ba bisa ka’ida ba. Maimakon su yi amfani da shi a matsayin tsoratarwa da baranzana ga wanda ya ki gaskiya ko ya yi jayayya da ita bayan sun tsayar masa da hujja, sai kawai su kashe duk wanda suka ga dama. Sannan amfaninsa shi ne sarrafa shi domin samar da kayayykin noma da motoci da jirage da babura da sauran kayan amfanin rayuwa da kuma tsayar da haddi a kan jama’a.
Don haka, ganin arahar makamai ba hujja ce da kowane mutum zai dauka ya halaka wanda ya ga dama da sunan addini ba, addinin Musulunci yana da ka’idoji a cikin komai na rayuwa, ciki har da jihadi. Don haka duk wanda ya dauki makami ya rika kashe wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, ba jihadi yake yi ba, maimakon haka yana bata sunan Musulunci ne. Yana yi wa makiya Musulunci aiki ne, ta hanyar hutar da su daga nuna wa duniya cewa wannan addini mai tsarki ba abin da yake bukata sai zubar da jini haka kawai. Allah Ya tsare mu.
5. Watsi da bidi’o’i da son rayuka:
Daga cikin hanyoyin tsare addini akwai watsi da bidi’o’i da son rayuka na daidaikunmu. Wajibi ne mu ajiye duk wani abu da bai da tushe da muka sanya a cikin wannan addini.
An karbo daga A’isha (Allah Ya kara mata yarda) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya kirkiri wani abu a cikin al’amarinmu wannan (addini) wanda bai daga cikinsa, to an mayar masa.” (Buhari a Kitabus Sulhu, Hadisi na 2697 da Muslim a Al’akdiyya, Hadisi na 1718).
Game da wannan Hadisi Imam An-Nawawi ya ce: “Wannan Hadisi yana da fa’ida mai girma daga cikin ka’idojin addini. Yana daga cikin maganganunsa masu hikima (SAW). A fili yake wajen mayar da kowace bidi’a ko kirkirarrun al’amura.” (Sharhus Sahihil Muslim, mujalladi na 12, shafi na 16).