Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al’umma (5)
Bayyanar bidi’o’i na cutar da addini, sukan haifar da bacewar hukunce-hukuncensa da dusashe kyansa. Kuma sababi na farko shi ke sabbaba bacewar shari’a, na biyu kuma na sabbaba bijirewa daga gare ta da rashin girmama ta, kuma wannan ne halin da ake ciki a yanzu, inda bidi’o’i suka yawaita suka zama jiki, suka zama abin […]
Bayyanar bidi’o’i na cutar da addini, sukan haifar da bacewar hukunce-hukuncensa da dusashe kyansa. Kuma sababi na farko shi ke sabbaba bacewar shari’a, na biyu kuma na sabbaba bijirewa daga gare ta da rashin girmama ta, kuma wannan ne halin da ake ciki a yanzu, inda bidi’o’i suka yawaita suka zama jiki, suka zama abin ado fiye da addinin kansa, suka maye gurbin addini a zukatan mutane da dama, suka zama su ne addinin da mutane suka fi jin dadin aikata su. Wadannan kuwa su ne hanyoyin da wadanda suka gabace mu (Yahudu da Nasara) suka bi har aka rasa shari’ar Annabawansu (AS), mutane suka bar addini. Domin karin bayani ana iya duba littafin Albid’ah: Asbabuha wa Misar, na Mahmud Shaltut shafi na 57 da Bi-Wasidatul Ilmus Usulil Bida’i na Aliyu Hassan Abdulhamid, shafi na 287.
6. Tsayar da haddin ridda:
Wata hanya ta kare addini da kyautata shi, ita ce ta tsayar da haddin ridda da sauran haddodi da suka shafi cin zarafin addini. An karbo daga Ibnu Abbas cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya canja addininsa ku kashe shi.) (Buhari, Kitabu Istitibatul Murtaddina wal Muharibina, Babu katlul Murtaddi wal Murtadda, Hadisi na 6922).
Wannan aiki ne na hukumar Musulunci ba na daidaikun jama’a ba. Don haka a wannan lokaci da galibin hukumomi suka kasance ballagazazzu marasa addini, nauyin kare wannan addini gwargwadon iko ya dawo kan al’ummar Musulmi, kare addinin kuwa zai fara ne da da’awa da wa’azi, in har hukuma ta nemi hana wannan sai a fara batun hijira, wadda a yanzu tasirinta takaitaccen ne sakamakon yadda Turawa suka kekketa duniyar Musulmi zuwa kasa-kasa, suka kuma sanya musu akidar ’yan kasanci.
Sannan a Musulunci ba a zama cikin gari ana sari-ka-noke ko a auka wa kowane mutum da sunan jihadi, saboda Musulunci bai lamunci a dauki rayukan jama’a a sanya cikin hadari ba.
Na biyu: Kyautata tsare rai:
1.Haramta yin ta’adda ga rayuka:
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi a kansa, kuma Ya la’ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azaba mai girma.” (k:4:93).
Ibnu Kasir ya ce: “Wannan tsoratarwa ce mai tsanani da gargadi mai karfi ga wanda ya aikata wannan zunubi mai girma, kuma an yi takarininsa da shirka ga Allah a ayoyi sama da dari a cikin Littafin Allah kamar inda Yake cewa: “Kuma wadanda ba su kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki…” (k:25:68). Da kuma fadinSa Madaukaki: “Ka ce: “Ku zo in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta.” Wajibi ne a kanku kada ku yi shirkin komai da Shi…” har zuwa inda Yake cewa: “kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, face da hakki.” (k:6:151). Ayoyi da hadisan da suke haramta kashe rai suna da yawa matuka.” (Tafsirul kur’anil Azim, juz’i na 1, shafi na 548).
Ibnu Hazam (RH) ya ce: “Babu zunubi a wurin Allah Madaukaki a bayan shirka da ya kai girman abubuwa biyu: Na farko: Barin Sallah ta farilla har lokacinta ya fita. Na biyu: kashe ran mumini ko mumina da gangan ba tare da hakki ba.” (Almuhalla, mujalladi na 10, shafi na 342).
2.Toshe kafafen da za su karfafa kisa:
Hakika shari’ar Musulunci ta kwadaitar kan toshe kafafen da za su jawo aukuwar fasadi, tare da bude wadanda za su karfafa zaman lafiya da maslaha a tsakanin jama’a. Sai ta haramta yin ta’adda a kan Musulmi da daukar makami domin yakarsu. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya dauki makami a kanmu (ya yake mu) to, ba ya daga cikinmu.” (Buhari a Kitabul Fitnu, Babin wanda ya dauki makami a kanmu, Hadisi na 707).
Ibnu Dakik Al-id ya ce: “A cikinsa akwai dalili kan haramci yakar Musulmi da tsanantawa kan haka.” (Fathul Bari, mujalladi na 13, shafi na 27).
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Zagin (ko aibata) Musulmi, fasikanci ne, kuma yakarsa (ko kashe) shi kafirci ne.” (Buhari a Kitabul Imani, Babin tsoron kada mumini ya bata aikinsa alhali bai sani ba, Hadisi na 48 da Muslim a Kitabul Iman, Hadisi na 116).
Hafiz Ibnu Hajar ya ce: “Kasancewar yaki ko kisa ya fi zagi ko aibatawa muni, saboda yana jawo zubar da jini, sai ya ambace shi da lafazi mafi tsanani daga fasikanci, wato kafirci. Sai dai ba ana nufin hakikanin kafrici wanda ke fitar da mutum daga Musulunci kacokan ba ne, a’a an jingina masa kafirci ne don kaiwa makura wajen yin gargadi.” (Fathul Bari, mujalladi na 1, shafi na 138).
Kuma malaman fikihu sun karfafa biyan diyya game da abin da ya shafi yin wani abu da ya sabbaba kisan kai.
Misali Ibnu kudama (RH) ya ce: “Ya wajaba a a dora biyan diyya kan sababin da ya jawo rasa rai, kamar yadda yake wajaba ga wanda ya yi kisan da hannu. Misali idan mutum ya tona rijiya a kan hanya, ba domin wata maslaha ga Musulmi ba, ko ya gina ta a filin da ba nasa ba kuma ba tare da izinin mai filin ba, ko ya sanya dutse ko karfe a kan hanya, ko ya jawo ruwa a cikinta, ko wani abu makamancin haka, sai wani mutum ya rasa ransa ko dabba ta rasa ranta ta dalilinsu, za a dora masa biyan diyya.” (Almugni, mujalladi na 12, shafi na 88).
3. kisasi a cikin kisan kai:
Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta a kanku, yin kisasi a cikin kasassu (wadanda aka kashe).” (k:2:178).
Ibnu Adiyya (RH) ya ce: “Yadda farlancin kisasi yake, shi ne wanda ya yi kisa an farlanta a kansa cewa, idan waliyyin wanda aka kashe ya mika al’amarinsa ga umarnin Allah kuma ya mika wuya ga yin kisasi, to shari’a ta yardar masa. Kuma lallai waliyyin an farlanta masa tsayawa a wurin kashe wanda ya kashe masa dan uwa, kuma an hana ta’addanci a kan waninsa kamar yadda Larabawa suke ta’addanci su yi ta kashe rayuka saboda kashe musu dan uwa daga mutanen wanda ya yi kisan. Kuma lallai an farlanta wa shugabanni tsayuwa wajen tabbatar da kisasi da tsayar da haddodi. Kuma ba a lizimta yin kisasi a ce dole ba, abin da ake lizimtawa shi ne dole ne wajen yin kisasin a tabbatar ba a wuce iyaka ba. Amma idan aka samu yarda cewa an jingine kisasin saboda biyan diyya ko afuwa, to hakan ya hallata. Ayar tana nuna cewa kisasi shi ne iyakar rashin hakuri da danne zuciya.” (Almuharrar Alwajiz, mujalladi na 1, shafi na 244).
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma kuna da rayuwa a cikin kisasi, ya ma’abuta hankula; tsammaninku, za ku yi takawa.” (k:2:179.
kattada (RH) ya ce: “Allah Ya sanya wannan kisasi ya zama rayuwa da gargadi da wa’azi ga ma’abuta wauta da jahilci daga cikin mutane. Domin mutane da yawa za su yi yunkurin halaka ran wasu ba domin suna tsoron kada kisasi ya hau kansu ba. Sai Allah Ya sanya kisasi ya zama katanga a tsakanin sashinsu da sashi. Allah bai taba umarni da wani abu ba, face wannan al’amari maslaha ne a duniya da Lahira. Kuma bai taba hani kan wani abu ba, face wannan al’amari fasadi ne a duniya da addini. Allah ne Mafi sanin abin da zai kyautata halittarSa.” (Jami’ul Bayan, mujalladi na 2, shafi na 119).