Lamarin Yunusa da Ese: Kukan kurciya ne ga ‘yan Arewa

Ganin yadda labarin Yunusa yellow dan asalin jihar Kano wadda ake zargi da laifin dauke yarinya Ese Oruru ‘yar asalin garin Bayelsa ba tare da izinin iyayenta ba yake kara watsuwa a duniya, da kuma yadda wasu daga cikin kafafen yada labarai, musamman ma na kudancin Nijeriya suke kara gishiri ta hanyar watsa labarin fiye […]

Lamarin Yunusa da Ese: Kukan kurciya ne ga ‘yan Arewa
Lamarin Yunusa da Ese: Kukan kurciya ne ga ‘yan Arewa

Ganin yadda labarin Yunusa yellow dan asalin jihar Kano wadda ake zargi da laifin dauke yarinya Ese Oruru ‘yar asalin garin Bayelsa ba tare da izinin iyayenta ba yake kara watsuwa a duniya, da kuma yadda wasu daga cikin kafafen yada labarai, musamman ma na kudancin Nijeriya suke kara gishiri ta hanyar watsa labarin fiye da yadda ya kamata da yadda suka dage wurin yada bangare daya na labarin ba tare da la’akari da dayan bangaren ba domin hakarsu ta cin ma ruwa, inda suka nuna cewa Yunusa ya yi laifi babba kuma shugabannin musulunci da sarakunan Arewa suna goyon bayansa.
Kodayake ba abin mamaki ba ne yadda mutanen kudu suka dauki labarin soyayya suka mai da shi maganar addini da kabilanci, musamman ganin yadda mutanen Nijeriya suke son addini, amma kuma ba sa son Allah. Domin kuwa a Nijeriya ne komai ake mayar da shi na addini ba tare da la’akari da yadda abin yake ba. A takaice dai, suna sanya kabilanci da addini a gaba da komai, duk kuwa da cewa ba sa yin addinin yadda ya kamata.
Duk da cewa dole ne ga iyaye masu hankali su nuna tashin hankalinsu idan suka ji diyar da suka haifi ta bar garinsu ta koma wata garin, sannan kuma ta canja addininta har ma ta yi aure. dole mutane za su tausaya musu,  sannan kuma a jajanta musu, ganin yadda suke neman su rasa ‘yar da suka haifa. Da kuma yadda aka dauko labarin bangaren iyayen Ese kawai a kai ta watsawa, kai ka ce an dauko jihar Bayelsa ne baki daya, ko kuma an dauko sarauniya daga Bayelsa an kai ta Kano.
Hakan ya sa wasu mutane suka fara zargin Yunusa da aikata babban laifin da ba haka ba ne, domin kuwa ko ni ma na yi rubuta a shafina na facebook a inda na nuna kuskuren Yunusa Yellow, sannan kuma na bukaci da a maida Ese garinsu, wanda ya jawo takaddama mai tsawo, sannan wani Abubakar Haruna yake cewa Ese ta musulunta ne kuma babu wanda ta tursasa ta.
Bayan haka, shi dai labarin Yunusa Yellow da Ese, a nawa ra’ayin, labari ne na soyayya wanda karshensa bai yi dadi ba, domin a wata wasika da ake tunanin Ese ta rubuta zuwa ga masoyinta Yunusa, ta nuna masa cewa lallai fa ya sani duk da cewa wasu wadanda ta kira su da Abubakar da Genedu da dantata suna sonta, amma duk lokacin da wani namiji yazo mata, sai Yunusa ya fado mata a rai, wanda hakan ya nuna yadda take tsananin son Yunusa. Sannan kuma a karshen wasikar take cewa, ko ma meye zai faru, ita dai tana son Yunusa, sannan ta kare wasikarta da cewa; daga masoyiyarka Rita, wacce aka fi sani da Ese.
Sannan kuma an nuna cewa Yunusa Yellow ya dade yana taya mahaifiyar Ese aiki a garin Bayelsa, duk da cewa shi bahaushe ne, sannan kuma ita mahaifiyar nata da babanta sun tabbatar cewa Yunusa mutumin kirki ne, domin sun yarda da shi sosai. Saboda soyayyar da ke tsakninsu da kuma tsoron ba za su ci ribar soyayyar ba a Bayelsa, sai suka yanke shawarar su tafi Kano domin ta musulunta sai ya aure ta. Sannan bayan ta je Kano, kamar yadda shugaban Hisbah Sheikh Daurawa ya nuna, ya ce iyayenta suna sane da cewa tana garin Kano, domin har sun zo domin su tafi da ita, bayan Hisbah ta ba su dammar yin haka, sai Ese ta nuna cewa ita ba za ta bi su su koma Bayelsa ba.
Bugu da kari, bayan zuwansu Kano, saboda tarbiya da adalci da sanin ya kamata na iyayen Yunusa, sai suka nuna rashin amincewarsu da abin da  ya aikata, domin haka ne suka kai maganar wurin Hakimi, wanda shi ma ya kai maganar wurin Mai martaba Sarkin Kano, shi kuma sarki sai ya ba da umurni da a maida ta Bayelsa, bayan ya samu bayani daga kwamitin shari’a na Kano. Abin mamaki kawai sai ga shi wasu suna cewa wai sarki ne ya ajiya ta a fadarsa domin ya tilasta mata ta musulunta. Wannan karyar da me ta yi kama?
 A karshe, duk da cewa labarin Yunusa da Ese labarin soyayya ne wanda karshensa bai yi dadi ba, ya kamata mu koyi darasi daga al’amarin, domin kuwa ana samun wadansu shugabannin addini da suke aikata alfasha, kamar wani wanda kwanan nan kotun koli ta tabbatar da hukuncin kisa a kansa domin aikata laifin kisan kai, amma sai dai a ambaci sunansa ba za ka ji an ambaci kabilarsa ko addininsa ba, ballanta ma a aibata su. Kuma  za ka ji an ce an samu kamfani jarirai inda ake tara yara mata ana musu ciki suna haihuwa ana biyansu.Irin wadannan misalan suna da yawa,  amma da wuya ka ji an ambaci kabila ko addinin masu aikatawa. To idan haka ne, masu iya magana suna cewa; kukan kurciya jawabi ne, mai hankali yake ganewa.
Daga Isiyaku Muhammed
Hayin Banki Kaduna
07036223691

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya