Lamido Barkindo ya yi susa inda ke kaikayi
Yanzu an shiga mako na uku daga cikin goma sha biyu da Shugaba Goodluck Jonathan ya diba ma wakilan taron kasa don tsara dabarun tserar da Najeriya daga masifun da ke addabarta a matsayin shawarwarin da za a aike da su ga Majalisar kasa don sarrafa su yadda ya kamata. Amma abin takaici game da […]
Yanzu an shiga mako na uku daga cikin goma sha biyu da Shugaba Goodluck Jonathan ya diba ma wakilan taron kasa don tsara dabarun tserar da Najeriya daga masifun da ke addabarta a matsayin shawarwarin da za a aike da su ga Majalisar kasa don sarrafa su yadda ya kamata. Amma abin takaici game da haka shi ne cikin makonnin nan uku ba wani abin kirki da aka tsinana, an tsaya ana ta ka-ce-na-ce kan batun yadda za a amince da batutuwan da aka yi muhawara a kai.
Baicin haka kuma akwai rade-radin cewa wasu wakilan, musamman ma daga yankunan Kudu-maso-Gabas da kuma na Kudu-Kudu na tsara dabarun kauce wa umurnin Shugaban kasa, wanda ya kira taron, na guje tattauna wasu batutuwa da ya haramta wa taron, musamman ma wadanda suka shafi hadin kan kasar nan ko ci gaba da kasancewarta dunkulalliya. An ce wadannan wakilan na ganin cewa tun da yanzu dama ta rigaya ta samu don tattauna batutuwan da ke kawo wa kasar nan cikas, to kuwa babu wani dalilin da zai sa za a kebe wasu al’amura , a ce ba za a waiwaye su ba alhali kuwa su ne ke yi wa kowa kaikayi ko dabaibayi, domin idan ba a yi haka ba, to ta yaya za a fahimci juna a kuma mance da dukkan bambance-bambancen da ke tsakanin al’ummomin kasar nan?
Bisa ga dukkan alamu dai sai an kai ruwa rana game da yunkurin da wasu kabilu ke yi na ganin cewa sai an aiwatar da wasu manufofin da suka dade suna luguiguitawa, wadanda kuma yin haka zai shafi hadin kai da zaman tarayyar da jama’ar kasar nan ke yi a halin yanzu. Alal misali wasu daga cikin wakilan shiyyar Kudu-maso-Gabas sun dage lallai sai an tattauna batun yankewar yankinsu don a dawo da Jamhuriyar Biafra, wasu kuma daga shiyyar Kudu-maso-Yamma sun dage a kan za su takulo batun bai wa kowace shiyya ko yankin kasar nan damar ballewa daga tarayyar jamhuriyar Najeriya don cin gashin kansa a karkashin wani sabon sunan da zai dace da buri ko manufarsa. Shi ya sa ma wakilan yankin Kudu-Kudu ke neman lallai sai a bullo da tsarin kowa-ya-kama-kifi-gorarsa, domin ta haka ne za su samu sukunin cin gajiyar dimbin arzikin man fetur din da ke jibge a yankinsu, su kadai, ba tare da sauran ’yan Najeriya ba, kuma idan har hakan ya ki samuwa, sai su balle daga kasar, su kafa tasu can daban.
A game da haka nan ana jin cewa akwai hannun wasu kasashen Yammacin Turai da kuma Amerika da ke son afkuwar haka, domin kuwa tun ba yau ne ba suke ta fafitikar ganin sun kafa wani tsarin da zai ba su damar girke rundunonin sojinsu a gabar tekun Guinea don jin dadin tatse arzikin man da ke kasashen da ke wannan dan tsukin da ya hada da Najeriya da Angola da Kamaru da kuma Gabon. A yanzu ma kasar Faransa ta rigaya ta kallafa ranta kan man fetur din da ake samu a yankin Tafkin Chadi, musamman a Najeriya da Chadi da Nijar da kuma wani dan zirin kasar Kamaru.
Ashe ke nan ana iya cewa wannan ne dalilan da suka hana kasarmu zama lafiya, kuma mutanen yankin Gabashi, wadanda Yahudu da Nasara ke hure wa kunne suke ta hankoron janyo gagarumar matsalar da za ta kara dagula al’amuran da za su yi sanadiyyar wargajewar kasar don su samu biyan bukatarsu. To shi ne a zauren taron kasa da ake yi Lamidon Adamawa, Dokta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa, daya daga cikin wakilan da kungiyar sarakunan gargajiya ta Najeriya suka tura can ya nakalci yadda bakunan wakilan waccan shiyyar suka karkata, har ma kuma ya fahimci irin miyaun da zai gangaro, ya kuma ce idan har sun tsokalo sama da kara, ta kuma fado kan jama’ar Najeriya, shi da sauran jama’arsa na da wurin zuwa don su buya, ba kamar wasu ba da ba su da wata makoma ko ingantacciyar mafita.
Wannan batu nasa abin a yi la’akari ne da shi, a kuma fara daukar matakan da za su samar da zabi mafi dacewa idan har take-taken wasu ’yan Najeriya ya jawo wargajewarta, domin kuwa bisa ga dukkan alamu inda aka dosa ke nan. Yin haka ya zama wajibi, domin ba lallai ba ne ’yan Arewa su zauna, ba su cikin wani kyakkyawan shiri, har a yi masu sakiyar da ba ruwa, wato a yi masu yankan kaunar da za ta fitar da su daga tarayyar Najeriya. A takaice dai ana iya cewa da bazar Arewa Najeriya ke rawa, kuma kada a manta cewa makekiyar kasar noma, mai cike da albarkatun ma’adinai da kuma wasu da ba a samu sukunin hako su ba, hade da dimbin jama’ar da suke yankin Arewa fiye da na wasu kasashen Afirka goma sha biyu, sun isa su zama jarin da zai taimaki Arewar tsayawa bisa kafafunta idan har ta kai sai kowa ya kama gabansa. Wannan ne ya sa sauran ’yan Kudu suka yi shiru, ba su tsattsagi ra’ayin Lamido Barkindo ba domin sun san cewa ba su kadai ne ke da hakkin furta wanan ra’ayin ba. Kuma ko ba komai, ya sosa wa inda ke wa kowa kaikayi.