Lamido Sanusi ya yi ƙarar Jonathan kan dakatar da shi
Gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shigar da kara yana kalubalantar dakatar da shi da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi.Lauyan Malam Sanusi Lamido, Cif Kola Awodein ne ya shigar da karar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.karar ta buƙaci kotun ta hana gwamnati daukar duk wani mataki […]
Gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shigar da kara yana kalubalantar dakatar da shi da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi.
Lauyan Malam Sanusi Lamido, Cif Kola Awodein ne ya shigar da karar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
karar ta buƙaci kotun ta hana gwamnati daukar duk wani mataki na aiwatar dakatarwar da aka yi wa Lamido Sanusi har sai an kammala shari’ar.
Ya kuma bukaci kotun ta ba da wani umarnin da zai hana Gwamnatin Tarayya hana shi, ko kawo masa cikas da nufin hana shi ci gaba da aikinsa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya.
Gwamnan Babban Bankin da aka dakatar ya ce, an dauki matakin dakatar da shi ne saboda ya tona salwantar wasu kudade da ya kamata a ce sun shiga Asusun Gwamnatin Tarayya.
A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaba Goodluck Jonathan ya ce, ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin ne da nufin ba da damar a binciki zargin aikata ba daidai ba da ake yi masa.
A tarkadar rantsuwar kotu domin karfafa bukatarsa Lamido Sanusi ya ce a kokarin sauke nauyin da ke kansa a matsayinsa na Gwamnan Babban Banki ya gano akwai gibi a adadin kudin da aka shiga Asusun Tarayya daga cinikin man fetur da aka gudanar a tsakanin watan Janairun 2012 zuwa Yulin 2013, kuma nuna damuwa da hakan ne ya sa ya sanar da Majalisar Dokoki ta kasa kan wannan gibi, domin ya shafi kudaden shiga na tarayyada kuma tattalin arzikin kasa.
Ya ce matakin da Shugaba Jonathan ya dauka na dakatar da shi daga mukaminsa an yi ne da manufar hukunta shi kan wannan fallasa. Ya ce yana kalubalantar Shugaba Jonathan ne kan dakatar da shi saboda bai tuntuba ko ya samu goyon bayan Majalisar Dattawa, bisa tattaunawarsa da sanatoci da dama ciki har da Sanata Bukola Saraki.
karar wadda aka shigar ranar Litinin da ta gabata har zuwa hada wannan rahoto tana sashin shigar da kararraki na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tana jiran a mika tag a alkalin da zai saurare ta.
A ranar Alhamis da ta gabata ce aka dakatar da Lamido Sanusi daga mukaminsa a daidai lokacin da yake halartar taron Gwamnonin Bankunan kasashen Afirka a Yamai ta kasar Nijar. Kuma yana dawowa jami’an tsaro na SSS suka yi masa tambayoyi a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas tare da kwace takardun tafiyarsa.
Dakatar da shi ta samu suka daga masana tattalin arziki da ’yan adawa ciki har da Majalisar Gwamnonin Najeriya, wadda ta ce dakatarwar da Jontahan ya yi ta saba wa tsarin mulki da dokar Babban Bankin ta shekarar 2007.