Lamido ya bar Sakataren Gwamnati da mika mulki a Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya mika ragamar mulkin jihar ga Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Alhaji Lawan Abdu babura, a matsayin Mukaddashin Gwamnan Jihar da zai rike ta na kwana tara kafin ya mika mulki ga zababben Gwamna Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar a ranar 29 ga watan Mayu. Gwamna Lamido wanda ya fice zuwa […]
Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya mika ragamar mulkin jihar ga Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Alhaji Lawan Abdu babura, a matsayin Mukaddashin Gwamnan Jihar da zai rike ta na kwana tara kafin ya mika mulki ga zababben Gwamna Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar a ranar 29 ga watan Mayu.
Gwamna Lamido wanda ya fice zuwa kasar Ingila domin a duba lafiyarsa, kafin ya fice sai da ya gana da duk wadanda ya kamata ya gana da su, sannan ya wucee kai-tsaye zuwa filin jirgin saman jiha da ke Fanisau ya hau jirgi ya yi tafiyarsa.
Gwamna Lamido ya ce kai-tsaye zai sauka a Landan don ganawa da likitansa, inda daga nan zai wuce Saudiyya domin yin Umara, kuma ba zai dawo ba sai bayan an mika mulki.
Gwamna Lamido ya ce zai caccaki gwamnati mai zuwa muddin ta yi abin da bai kamata ba, inda ya ce akwai bukatar jama’a su yi wa gwamnati mai zuwa addu’a domin mummunar addu’a ba a kan mutum daya take tsayawa ba tana shafar kowa, kuma ya hori jama’a su rika kyautata zato da fatan alheri ga gwamnati mai zuwa.
Lamido ya ce idan ya dawo zai raba rayuwarsa ne gida biyu rabi yana Kano daga Litinin zuwa Laraba, daga Alhamis zuwa Lahadi yana kauyensu Bamaina don ganawa da masoya da abokan arziki.
Manya da kananan jami’an gwamnati sun fashe da kuka a filin jirgin saman ciki har da Shugaban Majalisar Jihar Adamu Ahmed Sarawa da kwamashinonin da manyan sakatarori lokacin da Gwamna Lamido ke ban kwana da su.