Lamido ya zama maraya a siyasar Najeriya – Sani Zoro

Tsohon shugaban kungiyar ’Yan jarida ta kasa (NUJ) Alhaji Sani Muhammed Zoro ya ce ficewar da tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo daga Jam’iyyar PDP wani abin al’amari ne da ya dada wa jama’ar kasar nan rai, kuma hakan ya sa mutane irin su Gwamna Sule Lamido sun zama marayu a cikin siyasar Najeriya. Alhaji […]

Lamido ya zama maraya a siyasar Najeriya – Sani Zoro
Lamido ya zama maraya a siyasar Najeriya – Sani Zoro

Tsohon shugaban kungiyar ’Yan jarida ta kasa (NUJ) Alhaji Sani Muhammed Zoro ya ce ficewar da tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo daga Jam’iyyar PDP wani abin al’amari ne da ya dada wa jama’ar kasar nan rai, kuma hakan ya sa mutane irin su Gwamna Sule Lamido sun zama marayu a cikin siyasar Najeriya. Alhaji Sani Zoro ya fadi haka ne a hira ta waya da wakilinmu.

Alhaji Sani Zoro wanda ke takarar Majalisar Tarayya a karkashin Jam’iyyar APC daga Jihar Jigawa ya ce yana tausaya wa mutane irin su Gwamna Lamido a fagen siyasar Najeriya domin sun rasa uba yanzu sun zama marayu. “Yanzu Gwamna Lamido ya rasa alkibla ba ya da makoma a siyasar kasar nan domin bay a da madafar da ta wuce Obasanjo, kuma ga shi Obasanjo ya bar Jam’iyyar PDP. Don haka mafitar da ta dace da Gwamna Lamido ita ce ya fice daga jam’iyyar kamar yadda Obasanjo ya yi, kuma hakan ba zai yiwu ba saboda rashin gaskiyar da ya aikata wadda ta sa ya kasa ficewa daga jam’iyyar,” inji shi.
Alhaji Sani Zoro ya ce jam’iyyarsu ta APC tana kara habaka da karbuwa a jihar inda jama’a ke barin PDP suna shigowa jam’iyyar.
Ya shawarci Gwamna Lamido ya yada kwallon mangoro ya huta da kuad, domin Jam’iyyar APC a shirye take ta ba shi kariyar da ya kamata, kuma za ta karbe shi ba tare da nuna kyama ko bambancin manufa ba.