Lamido zai koma Jam’iyyar APC in… Inji Umar danjani
Alhaji Umar Muhammed danjani Hadeja dan marigayi Alhaji Muhammadu danjani Hadeja ne wani fitaccen dan Jam’iyyar NEPU da PRP. Umar wanda Mai ba Gwamnan Jihar Jigawa ne shawara kan harkokin dalibai da karatu, ya ce idan al’amari ya ki ci –ya ki cinyewa babu makawa Gwamna Sule Lamido zai koma Jam’iyyar APC. Ya shaida wa […]
Alhaji Umar Muhammed danjani Hadeja dan marigayi Alhaji Muhammadu danjani Hadeja ne wani fitaccen dan Jam’iyyar NEPU da PRP. Umar wanda Mai ba Gwamnan Jihar Jigawa ne shawara kan harkokin dalibai da karatu, ya ce idan al’amari ya ki ci –ya ki cinyewa babu makawa Gwamna Sule Lamido zai koma Jam’iyyar APC. Ya shaida wa Aminiya a tattaunawarsa da ita cewa rashin komawarsa a yanzu ba yana nufin ba ya tare da ’yan uwansa gwamnoni biyar ba ne, wani salo ne da dabarun siyasa.
Aminiya: Jama’a na yi wa Gwamna Lamido wata irin fassara saboda rashin komawarsa Jam’iyyyar APC da sauran gwamnoni biyar. Wadanda ba ’yan siyasa ba ne suna kallonsa a matsayin mayaudari me za ka ce?
danjani: A gaskiya masu fadar haka ba su yi wa Gwamna adalci ba, domin Gwamna Lamido da shi ne aka kafa Jam’iyyar PDP, saboda haka babu yadda za a yi a ce ya fice haka salin alin kamar yadda sauran gwamnonin biyar suka yi. Shi Lamido samunsa sukayi a cikin jam’iyyar domin su ne suka kafa ta a ganinmu barin jam’iyyar da Lamido ya ki yi daidai ne, domin sai yana ciki ne zai samu ikon yaki da su Bamanga kuma ya san sirrin halin da jam’iyyar take ciki in suka bari gaba daya ai babu yadda za a yi su san halin da ake ciki.
Matakin da gwamnonin suka dauka na barin jam’iyyar ba shi ne mafita ba domin in ka dauki Gwamnan Nyako da Gwamna Wamakko da Gwamnan Jihar Kwara ba ’yan ainisin Jam’iyyar PDP ba ne, gaba dayansu Gwamna Lamido ne kawai dan asalin Jam’iyyar PDP na ainihi. Kuma sanin kowa ne Lamido Janar ne a siyasar kasar nan saboda haka ba abu ne da zai bari a ce yana ciki yaki ya ci shi ba. Kuma kowa ya san Lamido ba ya barin yaki sai ya kai karshe ya ga iyakar yakin.
Gwamna Lamido mutum ne mai kwazo, kowa ya san ya samu Jihar Jigawa ana yi mana dariya cewar jihar kauyawa ce jihar matalauta da jihar da talauci ya yi wa tarnaki amma yanzu Jihar Jigawa tana cikin jihohin Najeriya da jama’a suke alfahari da ita wajen zaman lafiya da arziki da noma da kiwo. Don haka idan aka ce Lamido ne Shugaban kasa haka zai mayar da kasar nan batun tashin hankali da talauci zai zama tarihi domin wadannan abubuwa da suke damun jama’a wasu ne marasa kishi suka kirkiro su ba kasar ce haka ba.
Aminiya: Idan na fahimce ka kana nufin Gwamna Lamido ya zauna ne a cikin jam’iyyarku ta PDP domin ya ci gaba da yaki da Shugaba Jonathan ba sulhu suke yi ya koma PDP ba?
danjani: Haka ne mana ai shi dama kansa ya taba fada cewa shi da mutanensa wato su Kwankwaso da suka fita tafiyarsu daya ce domin su Gwamna Kwankwaso sun fita ne domin su yaki zaluncin da ake yi a cikin Jam’iyyar PDP, amma shi yana nan a cikinta da nufin ya ci gaba da yaki da jam’iyyar. Lamido yana nan a kan bakansa dole sai an yi adalci, muddin Shugaba Jonathan da Bamanga Tukur suna bukatar su ga daidai dole ne su tsaya su yi gaskiya.
Aminiya: Kana ganin za ku yi nasara a kan takarar da maigidanku Gwamna Lamido zai fito don neman shugabancin kasar nan a shekarar 2015?
danjani: Da yardar Allah kamar yadda Lamido ya samu Jihar Jigawa a mace murus zai hau kan mulkin kasar nan kuma haka zai gyara kasar nan ta koma kasa daya mai ’yanci ya fatattaki zalunci ya kori azzalumai, shi ne mutumin da muke ganin zai gyara kasar nan ta amsa sunanta a idon duniya.
Da yardar Allah in Gwamna Lamido ya zama Shugaban kasa zai tabbatar da adalci da nufin inganta rayuwar ’yan kasa da kuma gyara Najeriya lamarin da zai sa kowa ya ji dadi kamar yadda Lamido ya gyara Jihar Jigawa kowa yake jin dadinta yanzu.
Aminiya: Wasu na kallon kin komawar Gwamna Lamido zuwa APC kamar cin amana ce ya yi wa takwarorinsa gwamnonin biyar yaya kake kallon waccan maganar?
danjani: Wallahi lamarin ba haka ba ne duk wadanda suke waccan fassara ba su fahimci yadda lamarin yake ba. Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin kama ’ya’yan Gwamnan ne da kwamashinonin jihar da wasu mukarraban gwamnatin jihar da nufin ta ci mutuncinsa, kuma ba wai ya ki komawa Jam’iyyar APC ba ne saboda tsoron cin mutuncinsa da Gwamnatin Tarayya ta dauki aniyar yi ba, a’a ya yi haka ne domin wani salon siyasa. Gwamnatin Tarayya tana kallon cewa Lamido shi ne kamar shugaban wadancan gwamnoni biyar da suka fice suna ganin idan babu Lamido a cikin tafiyar tamkar sun karya gwamnonin biyar ne kuma ba za suyi nasara ba, shi ne ya sa suka dauki matakin karya shi ta fuskar tura masa jami’an EFCC su kama ’ya’yansa da wasu jami’an gwamnatin jihar.
Kowa ya san Gwamna Lamido ne uwa makarbiya wajen yi wa Bamanga Tukur da Jam’iyyar PDP tawaye, shi ya sa suke ganin yin hakan zai sa Lamido ya fada wa sauran gwamnonin biyar su ajiye makaman su daina yaki da Shugaba Jonathan. Har gobe Gwamna Lamido yana gaya wa Bamanga da Jonathan cewa Gwamnatin Tarayya da Jam’iyyar PDP ba sa aiwatar da komai daidai.
Aminiya: Yanzu kana nufin Gwamna Lamido ya koma tsohuwar PDP ke nan tunda abokan
tafiyarsa sun tafi sun bar shi?
danjani: Gwamna Lamido yana nan daram a cikin sabuwar PDP bai koma tsohuwar ba, kuma bai ajiye makamai ba yana ciki yana yaki da tsohuwar PDP, har yanzu ba shi kadai ba ne yake yaki da su Bamanga shi da su tsohon Gwamnan Jihar Gomba Sanata danjuma Goje da Gwamna Babangida Aliyu na Jihar Neja da sauransu.
Aminiya: Idan ba su yi nasara a kan abin da suka a gaba ba kasancewar sun zama ’yan tsirari yaya za su yi ke nan?
danjani:Ya zama dole su nemi mafita mana domin idan aka ga za a samu matsala dole ne daga karshe mu hade da wata jam’iyyar a cikin jam’iyyun kasar nan.
Aminiya: Wace jam’iyya ke nan za ku shiga in hakarku ba ta cimma ruwa ba?
danjani: Ba makawa za mu koma cikin Jam’iyyar APC, domin har yanzu muna magana da su kasancewar har yanzu muna tare da su kuma muna goyan bayan duk matakin da gwamnanmu ya dauka yazama dole Jam’iyyar PDP ko ta gyara ko kuma ta bare kowa ya rasa.