Lamidon Adamawa ya goyi bayan kowace jiha ta ci arzikinta

Lamidon Adamawa Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha kuma daya daga cikin sarakunan Arewa da ke halartar taron kasa ya bukaci a ba jihohin da ke da arzikin man fetur damar mallakar kudin man gaba dayansa.Lamidon ya kuma bukaci su ma jihohin da ba su da arzikin man, a ba su damar rike arzikin da suke da […]

Lamidon Adamawa ya goyi bayan kowace jiha ta ci arzikinta

Lamidon Adamawa Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha kuma daya daga cikin sarakunan Arewa da ke halartar taron kasa ya bukaci a ba jihohin da ke da arzikin man fetur damar mallakar kudin man gaba dayansa.
Lamidon ya kuma bukaci su ma jihohin da ba su da arzikin man, a ba su damar rike arzikin da suke da shi ciki har da filaye.
Mutanen Kudu maso Kudu da ake samun albarkatun mai a yankinsu a wurin taron sun yi ta murna da bayanin na Lamido.
Lamidon wanda ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa kan jawabin Shugaba Goodluck Jnathan ya ce:  “Tunda wasu sun bar ainihin batun da ya sa aka kira taron sun fara kiran a ba su damar iko da arzikinsu, to ni ma bari in baro ta, ina so a kyale jihohin da suke da albarkatun mai su rike kudin mansu gaba daya, sannan jihohin da ba su da mai a kyale su su mallake daukacin kasar da suke da ita.
Wannan yana nufin a mayar da filaye ga wadancan jihohi, kuma duk wanda yake son yin amfani da filin kasar ko gine-ginen da ke kan filayen a tilasta shi ya rika biyan kudin haya ga wadanann jihohi ko mamallakansu na gargajiya, kamar dai Abuja.” Wato wadanda ba ’yan Arewa ba da suke Abuja da wasu sassan Arewa su rika biyan kucin haya ga jihojin Arewa kan gine-ginen da suka yi a filayen.
Dagan an sai ya nuna rashin goyon baya ga kiraye-kirayen ba sarakuna matsayi a tsarin mulki.
Lamido ya shawarci maha-larta taron su tsaya kan jawabin Shugaba Jonathan su guji kwai-kwayon kasashen Yamma da suke cewa ba su da abokan gaba na dindindin, sai dai bukatu na dindindin wadanda suke yada al’adar aure a tsakanin jinsi daya.
A kwanakkin baya ma Lamidon ya yi wasu kalamai a wurin taron inda ya ce shi da jama’arsa ba su tsoron Najeriya ta wargaje bayan da wasu wakilan taron suka fara nuna wa Arewa yatsa, suna bukatar a wargaza kasar kowa ya kama gabansa.