Lampard ne zai horar da Chelsea – Harry Redknapp

Tsohon kocin kulob din Tottenham da ke Ingila Hary Redknapp ya yi hasashen tsohon kyaftin din Chelsea, Frank Lampard ne zai zama kocin kulob din kafin a fara kaka mai zuwa. Redknapp wanda ya horar da kulob da dama a Ingila da suka hada da Tottenham da Postmouth da Kueens Park Rangers da Southampton da […]

Lampard ne zai horar da Chelsea – Harry Redknapp

Tsohon kocin kulob din Tottenham da ke Ingila Hary Redknapp ya yi hasashen tsohon kyaftin din Chelsea, Frank Lampard ne zai zama kocin kulob din kafin a fara kaka mai zuwa.

Redknapp wanda ya horar da kulob da dama a Ingila da suka hada da Tottenham da Postmouth da Kueens Park Rangers da Southampton da kuma West Ham United ya ce a ra’ayinsa babu wanda ya fi dacewa ya zama kocin Chelsea fiye da Lampard.

Ya fadi haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake hira da kafar watsa labaran wasanni ta BBC Radio 5 libe.

Frank Lampard dai ya lashe Kofin Firimiya sau uku da Kofin Zakarun Turai sau daya a lokacin da yake yin kwallo a Chelsea.

Bayan ya yi ritaya  sai ya koma kocin kulob din Derby County da ke buga gasar rukunin ’yan dagaji a Ingila a bara, kuma alamu sun nuna zai maye gurbin tsohon kocin Chelsea Sarri da ya canja sheka zuwa kulob din Jubentus a makon jiya.

Yanzu haka Lampard yana  da shekara 40.