Langar ligidin Lagad

Zamanin da nake biye allona in wanke, ni da abokaina mun saba sayen hanjin ligidi a wajen wata tsohuwa Iya. Yau kuma sai ga shi uwargida Lagad, wadda ke jagorantar ligidin lamunin duniya ta gangaro fadar tsaunin Aso, inda ta gana da Baban-burin-huriyya, ta kuma yi kokarin sauke masa langarta ta hanjin ligidin, tun da […]

Langar ligidin Lagad
Langar ligidin Lagad

Zamanin da nake biye allona in wanke, ni da abokaina mun saba sayen hanjin ligidi a wajen wata tsohuwa Iya. Yau kuma sai ga shi uwargida Lagad, wadda ke jagorantar ligidin lamunin duniya ta gangaro fadar tsaunin Aso, inda ta gana da Baban-burin-huriyya, ta kuma yi kokarin sauke masa langarta ta hanjin ligidin, tun da Malam Mai yaren Hau-hau wajen hawansa ya ce “bashi hanji ne,” sai ta dan difara masa lamunin langar Ladidi da Lamunde; Idan muka ji dadi, wata rana kuma a sha wuya.
Haurobiyawa, masu karatun bobo da kwanbom bokoko ko ’yan makarantar allo, kowa ya san mun sha hanjin ligidi, musamman wanda ake tsikara shi a tsinke, kamar wata alawar a ci duniya da tsinke. Lallai a da mun ci duniyarmu da tsinke, amma lokacin da Baban -Haurobiya na kan dutse Jihar Ni-na-ja a birnin Mina-mina ya ciwo hanjin bashin hukumar lamuni ta duniya, daga nan muka jigata, bayan mun kwashi lagwada. Don haka mahukuntan Haurobiya kada ku bari uwargida Lagad ta sauke muku langarta ta hanjin ligidi.
’Yan makaranta ba na fargabar ko hanjin ligidin da ke cikin langar uwargida Lagad zai lallaga mu, a’a. Hasalima ‘a rashin tayi akan bar arha.’ Domin na tuna a shekara ta dubu kramin lauje da sili da  karamin lauje da muka dauki hanyar tafiya birnin Tagadas da ke kasr Niyyar-jari, sai muka sauka a Jihar Zindar, inda muka kira wata sayar da kayan dundume kururu da ke dauke da fanteka a ka. Sai muka tambayeta ko me kike dauyke da shi, sai kuwa ta ce mana “maka da malku.” Nan take wani abokin tafiyar mu ya dora hannu a ka, ya ce, “ai ba za mu iya dundume kururun mu da wann ba.” Sai ka samui wani mai hankali a kwanyarsa, ya bukaci lallai ta sauke domin mu tantance. Da bude fantekar da ke kana don gari, ai sai muka hanyo nannadaddiyar macaroni da romon kan akuya da kafafu. Sai kawai na yanke cewa, ai za mu iya make ’yar Gusau (wato Jihar Zaman-fara mai kulub-kulub a tumbi), malku kuwa za mu iya m,ululluke kowane loko da ’yar Gusau ke addabar mu a cikin kururu. Nan take muka saya muka biya, har ma muka nuna mata wasu daga cikin ayarin mu da ke laluben abin Karin kumallo.
Abin da kawai nike son nusar da mu shi ne, uwargida Lagad ta sauke langarda mu gani, idan akwai abin saye, mu saya mu biya, idan kuwa babu, sai mu ce, “Mai-duka ya bayar da sa’ar kasuwa.”
Batu na ingarman karafa, ita kanta uwargida Lagad ta fahimci hanjin ligidin tab a zai samu kasuwa ba, musamman ma idan an gindaya sharuddan azaftar da talakawa da sasari, ta yadda za a riga jan su kamar ja ni talau. Ita kanta uwargida Lagad da ta fahinci hanjin ligidinta ba dzai yi kasuwa ba a wannan karon, sai kawai ta furta cewa, kasar Haurobiya ba ta bukatar lamunin hanjin ligidi, kuma ko ta koma da langarta, abin da kawai take shawartar al’ummar kasar nan, shin me su tabbatar da kafuwar jagorancimutane nagargaru, wadanda ba za su jefa mu cikin garari ba.
Batu uwargida Lagad ya zama dutse, domin ta tabbtar da cewa, ba lamunin hanjin ligidi muke bukata ba, illa shugabanci nagargaru, amma ban da tafiyar kunkuru; kodayake na ji Baba na cewa, shi ba ya son ya zura da gudu don kada ya yi kuskure. Lallai Baba a kara wuta.
Ni ziyarar uwargida Lagad dauke da langar hanjin ligidinta bai dada ni da kasa ba. Domin ko ba komai ta tabbatar da cewa, idan har muka mara wa Baban mu baya, ya kwato dimbin dukiyar da jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka yi watandarta, musamman dan abin da Kanari Samun-Bom-da-Sauki ya rika difara wa su Baffan-rawa da tsoho Tunku Ya-kasa da Fuffuken-fan-kan-fayau; ga su Mace-da-zani da Santala kwaiduwa da tarin sauran miyagu da suka wawure rabon su, suka arce.
Sannan akwai wadanda suka haure da haraji. Don haka nake son ganin an karbo mana Harajinmu na Hauro tiren-taliya da ’yan mutsa-mutsai a wurin Maman-tine, tun kafin ta haure da shi a cikin kurtun Magana na halo-alalo. Kodayake na ji Jinjinniyar Dodorido tana cewa, Ayo! Ayo!!, shi ken an miyar Maman-tine sai ta zama ta ayayoyo.
Lallai masu koyon watsatsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin amintacciyar Jaridar kasar Haurobiya, wajibi ne ku fasko cewa, hatta Belin-auta da gwamnati ta yi a kwanakin da suka arce, ya kamata ta dan ja da baya domin kada a karke da Billen-wauta. Mu kuwa gama-garin al’umma mu koyi ririta abin hannu, ‘wadda duk ba ta yi gashin wance, kada ta sake tace za ta yi kitson wance,” a cewar Malam Mai yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa ba.
Uwargida Lagad ta yi mursisi za ta lallaga mana sisi. Ina dai fatan ba za ta yi laga-laga da mu ba. Saboda haka akwai bukatar mu lallaga wa ’yan fansho sulallan su da aka sulale da su. ‘’Yan kwadago kuwa na bukatar a saukaka hanyoyin lalubern kadago tun kafin wulwulawar agogo. Su kuwa masu hada-hadar kasuwanci wajibi ne a daina kaso-kason wawanci. Masu sana’ar na-duke da limbu-limbu cikin lambu kada ku bar ’yar Gusau ta jefa mu cikin lambatu. Ni dai na bayar da sautu, ya kamata in daina surutu rututu kmar Kamfnain Dillancin Labarai na Reuters. Da fatan kowa ya je Gano, watakila ma mu tsallaka zuwa kasar Ghana mu yi wo gane-gane.
Haurobiyawa mu yi aikin kwarai, kada mu daidaita kasar mu. Don haka wajibi ne mu tallafa wa Baban-burin-huriyya ya aiwatar da baje-kolin shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama; mu tabbatar da an aiwatar da tsarin adana damin Hauro na lalita sili don gudun kada a sulale da sulalla. Uwa-uba, mu barbada saman-dagarin samarin kusu a ramukan ’yan matan jaba da gafiya, ta yadda ba sai an turo Iro mugun madambaci ya hana magu-magu ba. Da zarar mun aiwatar da wadannan dabarbaru da makaranta ta bijiro da su, ina ganin za mu iya bugun kirji mu ce wa Uwargida Lagad “Langar hanjin ligidin da kike dauke da shi, sai a kai kai kasuwa, ko kuma a’a, a bari mun gode.