An sace kayan babban layin lantarkin Lokoja-Gwagwalada

Wuta ta ɗauke gaba ɗaya a babban layin lantarki na Lokoja zuwa Abuja a yayin da injiniyoyin Kamfanin TCN suke ƙoƙarin gyara bayan ɓata-gari sun lalata shi

An sace kayan babban layin lantarkin Lokoja-Gwagwalada

Turakun Wutar Lantarkin da Matashin ya rataye kansa

Babban layin wutar lantarki mai ƙarfin 330kV da ya taso daga Lokoja zuwa Gwagwalada ya lalace, lamarin da ya jefa yankin cikin duhu.

Kamfanin Samar da Lantarki na Kasa (TCN) ya tabbatar cewa lamarin ya katse wuta a manyan turakun lantarki na T306 da T307da T308 tun ranar Asabar.

Kakakin Kamfanin TCN, Ndidi Mbah, ta ce ɓata-gari da ba a san ko su wane ne be suka lalata babban layin wutar.

Ta bayyana cewa tun ranar Asabar da abin ga auku injiniyoyin kamfanin suka yi ƙoƙarin gyara wutar, amma sai ta ɗauke.

Ta ce a yayin bincike daga bisani injiniyoyin suka gano ɓata-garin sun yi awon gaba da kayan lantarkin layin guda biyu.

Sai dai ta ce kasancewar layin mai fuska biyu ne, har yanzu kamfanin na ƙoƙarin samar da wuta ta ɗaya fuskar da kuma maye gurbin ɗayan da aka sace kayansa.

Ta kuma koka bisa yadda a baya-bayan nan bata-gari ke lalata wa da sace muhimman na’urorin samar da wutar lantarki.

Kotu ta kori karar neman hana dalibai sanya hijabi

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya