Lantarki: Za a gina babbar tashar ‘Sola’ a kowace jiha a Arewa

fara tattaunawa da ’yan kwangila kan yiwuwar samar da mewat 100 na wutar lantarki mai amfani da hasken rana a duk jihar da ke Arewacin Nijeriya.

Lantarki: Za a gina babbar tashar ‘Sola’ a kowace jiha a Arewa

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta gina babbar tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kowace jiha da ke Arewacin Nijeriya.

Ministan ya ce gwamnatin ta fara tattaunawa da ’yan kwangila kan yiwuwar samar da mewat 100 na wutar lantarki mai amfani da hasken rana a duk jihar da ke yankin, duba da albarkar hasken rana da Allah Ya hore wa yankin.

Adebayo ya ce za a gina tashoshin ne da nufin tabbatar da samuwar tsayayyiya kuma wadatacciyar wutar lantarki a fadin yankin.

Ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Tinubu kan lalacewar wutar yankin na kimanin kwanaki 10.

Ministan ya bayyana cewa Tinubu ya umarci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro su bayar da duk tsaron da ya kamata domin gyara wutar Arewar.

Yankin Arewa ya kwashe sama da mako guda cikin duhu sakamakon lalacewar babban layin lantarki na Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ke kawo wuta zuwa yankin.

Kamfanin Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya bayyana cewa ’yan ta’adda ne suka lalata layin wutar, kuma isa wurin na domin aikin na da matukar hadari, amma yana aiki da hukumomin tsaro domin bayar da kariya ga ma’aikata domin gyara wutar.

Adelabu, ya kara da cewa Majalisar Zartaswa ta Qasa ta amince a sabunta tare da kara karfin layin wutan na Shiroro zuwa Kaduna wanda shi ne mafi dadewa a Nijeriya.

Ya ba wa al’ummar yankin hakuri game da lalacewar wutar, yana mai ba da tabbacin cewa nan da kwanaki biyar masu zuwa za gyara ta.

Ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin ganin ba a caje su kudin wutar da ba su sha ba a tsawon lokaci, kuma zai tattauna da Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) da kamfanonin rarraba wutar, a game da hakan.