Larabcin Bahadeje

Wani Bahadeje ne ya je Makka sai ya je ya sayi jallabiya. Da ya je gida ya gwada sai ya ga ta matse shi ta sama, ta kasa kuma ta bude. Ga shi kuma bai iya Larabci ba, sai ya koma wajen Balaraben nan mai saida kaya ya ce masa: “Jallabiyar da na saya wajenka […]

Larabcin Bahadeje
Larabcin Bahadeje

Wani Bahadeje ne ya je Makka sai ya je ya sayi jallabiya. Da ya je gida ya gwada sai ya ga ta matse shi ta sama, ta kasa kuma ta bude. Ga shi kuma bai iya Larabci ba, sai ya koma wajen Balaraben nan mai saida kaya ya ce masa: “Jallabiyar da na saya wajenka ta sama ta shake ni, ta kasa ta yi mini fadi.” Balarabe bai gane ba sai ya sake ce masa: “yaa akhi, wa izassama’un shakkat, wa izal ardi falalat.”
Daga Sagir Musbahu Daura Dole, 08095597525