Larry: Kyanwar da ta yi zamani da Firaministocin Birtaniya 4
An ga kwanwar ta je tarbar sabuwar Firaminista
Wata kyanwa mai suna Larry da ta yi zamani da Firaministocin Birtaniya guda uku a ranar Talata ta marabci Firayi Minista ta hudu, Liz Truss.
An ga kyanwar na jiran Liz Truss bayan da iyalan tsohon Firaminista Boris Johnson suka tattara komatsansu suka yi ban-kwana da Gidan Gwamnati da ke Downing Street, domin Liz Truss da iyalanta su shige ciki don fara nata mulkin.
Kyanwa Lary mai shekara 15, wadda ba mallakin kowa ba ce, ta zama babbar kyanwar gidan Firaminstan Birtaniya, kamar yadda kafar labarai ta Reuters ta ruwaito.