Launukan Soyayyar Ma’aurata
Soyayya ta kasu kashi daban-daban dangane da dan tsiron da ya shuka ta tun farko da kuma yadda aka gudanar da ita yayin da take girma da kuma irin sakamakon da ake sa ran samu daga gare ta. A jimlace, soyayyar auratayya tana da launauka guda biyu: cikakkiyar soyayya da kuma sarkakkiyar soyayya.1. Cikakkiyar SoyayyaIta […]
Soyayya ta kasu kashi daban-daban dangane da dan tsiron da ya shuka ta tun farko da kuma yadda aka gudanar da ita yayin da take girma da kuma irin sakamakon da ake sa ran samu daga gare ta. A jimlace, soyayyar auratayya tana da launauka guda biyu: cikakkiyar soyayya da kuma sarkakkiyar soyayya.
1. Cikakkiyar Soyayya
Ita ce kammalalliyar soyayya da ya kasance komai ya ji a cikinta; Ita ce soyayyar da ya kamata a ce kowane aure a kanta yake tafiya; ita ce soyayya mai cike da so, kauna, rahma da tausayin juna; ita ce soyayyar da ke cike da shakuwa, fahimtar juna, mutunta juna da sha’awar juna; ita ce wacce ta kunshi dukkan mafi kyawon sinadaran soyayyar nan guda hudu da bayaninsu ya gabata. Dadin dacewa da cikakkiya kuma kammalalliyar soyayya, dadi ne da babu irinsa a zuciyar dan Adam; yana daga ruhin dan Adam zuwa ga kololuwar farin ciki; don haka babban al’amari ne da ya kamata dukan ma’aurata su dage ga rike shi da kyau; ya zama samun irin soyyaya shi ne burinsu; su rike shi kamar wani muhimmin kasuwanci mai cike arziki mai yawa; kar su bari jarinsu a wannan kasuwanci ya karye, in ma ya karye su yi dukkan kokarin da ya kamata don kara samun jarin zubawa don guje ma kasancewa cikin kuncin kishiyar hakan a rayuwar aurensu. Da fatan Allah Ya hore ma dukkan ma’aurata wannan kyakkyawar soyayya, amin.
2. Sarkakkiyar Soyayya
Ita ce soyayya da ba ta amfanar ma’aurata, cikakken amfani; ita ce soyayyar da ke takurawa ga duka ko daya daga cikin ma’aurata; ita ce gurguwar soyayya mai nakasun biyu ko ukku daga cikin sinadaran da suka gina soyayya. Ita ce soyayya mai cike rashin fahimtar juna, yawan fadace-fadace, zargin juna; rashin yi ma juna uzuri; munana zato ga juna.; ita ce soyayyar da ba ta ba da yabanyar jin dadi da kwanciyar hankali. Ita ce soyayyar da ke nutsar da ma’aurata cikin ramin kunci da tashin hankali; ita ce fankon soyayyar da ba shakuwa, ba tausayi a cikinta; mai cike da dacin rai, jin zafin juna da kasancewa cikin halin kaka-nika-yi.
Soyayya na iya sarkewa a dalilin matsaloli daga ma’auratan dukansu ko daga bangare dayansu; yawancin matsalolin nan suna fadowa cikin soyayya ne bayan aure, kasancewarsu cikin aure ba shi ne ke sa soyayya ta zama sarkakkiya ba, illa dai yadda ma’aurata suka fuskanci matsalolin ne ke ruguza ko gina soyayyarsu. Ya kamata ma’aurata su fahimci cewa ba sai ana jin dadin juna kadai ake soyayya ba, ana soyayya a kowane irin lokaci ko yanayi; na tsanani da bacin rai, da kuma lokacin farin ciki da jin dadin rai. Rikon wannan gurguwar fahimta, ta cewa sai ana cikin dadin rai ake son juna, shi ke sa soyayya ta zama sarkakkiya mai cike da matsaloli. Don haka yana da matukar alfanu ga ma’aurata su fahimci yanayin motar soyayyarsu don su san yadda za su tuka ta har ta kai su ga gacin jin dadi da kwanciyar hankali cikin rayuwar aurensu. Da fatan Allah Ya cire dukkan wata sarkewa da nakasar da ke cikin soyayyar dukkan ma’aurata, amin.
Ku Fahimci Soyayya:
Yana da mataukar alfanu ga ma’aurata su fahimci tsantsar ma’anar kalmar soyayya. Sani da fahimtar kalmar soyayya a asalin ma’anarta, zai taimaka ga ma’auratan da ke sha’awar cika rayuwar aurensu da soyayya (samun) saukin yin hakan. Soyayya kalmar aikatau ce, kuma aikatau din ma na jam’i, watau wani abu da mutum biyu ko sama da haka ke yi, amma ba mutum daya ba; sannan kuma kalmar soyayya aikatau dinta mai gudana ne a kodayaushe, ba tsayawa ba dakatawa; watau da an fadi kalmar soyayya, an san wani abu ne da mutum biyu ke aikatar da shi a kodayaushe. Kamar kalmar ‘sayayya’ ce, ba ta yiwo mutum daya ya yi sayayya da kanshi, ya saida ma kanshi, dole sai akwai mai saye da mai sayarwa; duka da mai saye da mai sayarwan nan kowa zai amfana daga wannan sayayya kuma kowa zai samu biyan bukata. To haka soyayya take, kafin ta yi amfani ga ma’aurata, kuma su more ta, morewa mai kyau, dole sai su duka sun sa hannun jari a cikinta; ba uwargida kadai za ta yi ta soyance maigida ba, yana amsa amma bai mayarwa; komin yake jin dadin haka, in zai mayar irin yadda ake nuna masa ko fiye da haka, to sai ya fi jin dadinta sama da a ce shi ne zai yi ta amsa, ba maidawa. Haka ma abin yake ga uwargida, komin take jin dadin yadda take juya mijinta, to in za ta ba shi dama, shi ma ya rika juya ta, to abin sai ya fi mata dadi da armashi.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba, inshaAllah. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.