Lauya ta daba wa mijinta wuka ya mutu
Mai shari’a a kotun majistare ta Jihar Oyo, Kehinde Durosaro ta tsayar da ranar Talata mai zuwa, domin ci gaba da sauraron karar da Kwamishinan ’yan sanda na jihar ya kai Lauya Yewande Oyediran, da ake tuhuma da laifin kashe mijinta mai suna Oyelowo Oyediran, ta hanyar daba masa wuka a sassan jikinsa a lokacin […]
Mai shari’a a kotun majistare ta Jihar Oyo, Kehinde Durosaro ta tsayar da ranar Talata mai zuwa, domin ci gaba da sauraron karar da Kwamishinan ’yan sanda na jihar ya kai Lauya Yewande Oyediran, da ake tuhuma da laifin kashe mijinta mai suna Oyelowo Oyediran, ta hanyar daba masa wuka a sassan jikinsa a lokacin da suka kaure da fada sau biyu a cikin dare, a gidan da suke zaune a unguwar Akobo, Ibadan a ranar Talatar makon jiya.
Kamar yadda al’amarin ya faru, lokacin da aka sanar wa Pa Yaya Oyewole, wanda shi ne uban goyon mamacin kuma surukin ita wadda ake tuhuma labarin mutuwar dan nasa, nan take ya fadi kasa kuma rai ya yi halinsa.
Shi dai mamacin, bincike ya tabbatar da cewa dan kasuwa ne shi da yake tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya daban-daban. Matar tasa, wacce lauya ce kuma diyar Babban-Sakatare mai ritaya ce a Jihar Oyo, Olatinwo Adegbenro Fatoki, ta caka masa wuka ne a kafada, saboda ta samu labarin yana da da a tare da wata matar ta daban da yake aure.
Tun da farko dai mamacin yana zaune ne a kasar Paris, kafin daga bisani ya dawo gida Najeriya a 2014, inda suka yi aure da ita Yewande, wacce lauya ce da ke aiki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Oyo.
Kamar yadda wani makwabcinsu, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya, ya ce ma’auratan sun dauki lokaci da dare suna rikici a gidansu.
“Kafin su kwanta barci, ma’auratan sun samu sabani saboda shi mijin yana shirin tafiya harkokin kasuwancinsa kasashen Turai, amma ya ce zai biya kasar da matarsa daya take, inda zai gana da dansa da ke can. Wannan kishi ne ya kama matar tasa, har ta kai ga caka masa wuka. Mai gidan da suke haya ne ma ya shiga tsakani, inda ya kai shi asibiti, bayan an yi masa magani ya dawo gida ya kwanta.
“Can cikin tsakar dare sai muka ji Oyelowo yana kakari kuma da muka je gidan sai muka same shi jini yana fita daga wuyansa da bakinsa. Ya shaida mana cewa matar tasa ce ta sake yin amfanin da wuka ta soka masa, a lokacin da yake barci. An yi kokarin kai shi asibiti amma ana zuwa ma suka tabbatar da cewa ya mutu.” Inji shi.
’Yan sanda sun kama Lauya Yewande ne a ranar Larabar makon jiya, da suka kammala bincike suka gurfanar da ita a gaban kotun majistare da ke Iyaganku, Ibadan a ranar Juma’a, inda aka tuhume ta da laifin daba wa mijinta wuka a wuya da sassan jikinsa, wanda haka ya yi sanadin mutuwarsa.
Lauyan da yake kare matar da ake tuhuma, Mista Seun Abimbola, ya roki kotun da ta bayar da umarnin tsare wacce yake karewa a ofishin ’yan sanda wanda mai shari’a Kehinde Durosaro ta ki amincewa da wannan bukata kuma ta bayar da umarnin a garkame ta a gidan yari na Agodi da ke Ibadan har zuwa ranar 16 ga watan da muke ciki, domin ci gaba da sauraron karar.