Lauya ya kai karar Italiya da Isra’ila kan laifin gicciye Yesu

Wani lauya a kasar Kenya, Mista Dola Indidis, ya kai karar kasashen Italiya da Isra’ila, don su soke hukuncin gicciye Yesu Almasihu. Lauyan ya jajirce kan cewa wannan laifin da aka aikata yah au kan kasashen biyu, kamar yadda Jaridar the Christian Poast ta ruwaitio.Mista Indidis, dan darikar Roman Katolika ne, kuma tsohon mai amgana […]

Lauya ya kai karar Italiya da Isra’ila kan laifin gicciye Yesu

Lauya Indidis wanda ya kai Isra’ila da Italiya kara kan laifin gicciye Yesu AlmasihuWani lauya a kasar Kenya, Mista Dola Indidis, ya kai karar kasashen Italiya da Isra’ila, don su soke hukuncin gicciye Yesu Almasihu. Lauyan ya jajirce kan cewa wannan laifin da aka aikata yah au kan kasashen biyu, kamar yadda Jaridar the Christian Poast ta ruwaitio.
Mista Indidis, dan darikar Roman Katolika ne, kuma tsohon mai amgana da yawun Hukumar Shari’a ta kasar Kenya, ya gabatar da kara ne kan bukatar kotun duniya ta ICJ, wadda ke karkashin Majalisar dinkin Duniya da ke birnin Hague a kasar Netherlands.
Ya gabatar da karar tuhumar Pontius Pilate, wasu manyan shugabannin Yahudawa da Sarki Herod dfa Tiberus (Sarkin Rum a tsakanin shekaru 42 kafin hahihuwar Ananbi Isa zuwa shekara 37 bayan almasihu); don haka yake tuhumar Jamhuriyar Italiya da kasar Isra’ila.
“Na gabatar da wannan karar ne don aikina ne in kare mutuncin Yesu, don haka na tafi kotun duniya ta ICJ, don neman tabbatar da adalci kan mutumin Nazareth,” a cewar Indidis, kamar yadda ya bayyana wa jaridar the Nairobian, a wata ganawa da ta yi da shi.
“Wannan cin mutunci na nuna wariya ya keta hakkinsa na dan Adam, ta hanyar tafka wautar shari’a, da amfani da mukami wajen aikata son rai,” inji shi.
Kotun duniya ta ICJ za ta water wnai lokaci na sauraren karar Indidis, sai dai ta yi nuni da akwai wata ’yar  karamar matsala ce. “Kotun duniya ta ICJ ba ta da hurumin yanke hukunci kan irin wannan karar,” a cewar mai amgana da yawunta, kamar yadda ya bayyana wa shafin sadarwar harkokin shari’a na Legal Cheek.
“Kotun ICJ na warware matsaloli ne da suka hada da rikice-rikice tsakanin kasashe. Don haka ba ma daidai ba ne mu saurari irin wannan karar,” inji shi. Mista Indidis ya dade yana son gabatatr da wannan karar. Domin a shekarar 2007 ya gabatar da karar a gaban Babbar Kotun Kenya da ke Nairobi, amma aka yi watsi da ita, domin ba ta da tushe a doka, musamman ganin wadanda Indisis ke yunkurin gurfanarwa sun mutu  shekara dubu biyu da suka gabata.
Anthea Robert, Farfesan shari’a a Jami’ar Kolombiya ta Amurka, ta bayyana shafin sadarwar harkokin siyasa na Mujallar Times, cewa: “Kotun duniya ta ICJ ba ta hurumin suararen wannan karar, domin tana warware matsaloli ne a tsakanin kasashen duniya, musamman ma ganuin cewa wannan karar ba wata kasa c eta gabatar da karar ba.”

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan