Lauyan bogi ya shiga komar ’yan sanda a Ogun

Wani lauyan bogi mai shekara 47 mai suna Balogun Ayodele ya shiga komar ’yan sandan Jihar Ogun bayan da ya ziyarci Kotun Majistare ta Ilaro da ke jihar da zimmar kare wani da ake yi wa shari’a a kotun. Dubun lauyan bogin Balogun Ayodele ta cika ne bayan da alkalin kotun ya lura da yanayin […]

Lauyan bogi ya shiga komar ’yan sanda a Ogun

Lauyan bogi Balogun Ayodele

Wani lauyan bogi mai shekara 47 mai suna Balogun Ayodele ya shiga komar ’yan sandan Jihar Ogun bayan da ya ziyarci Kotun Majistare ta Ilaro da ke jihar da zimmar kare wani da ake yi wa shari’a a kotun.

Dubun lauyan bogin Balogun Ayodele ta cika ne bayan da alkalin kotun ya lura da yanayin shigar lauyan bogin da kuma yadda yake bayanansa a gaban mai shari’ar, hakan ne ya sanya alkalin ya yi ta yi masa tambayoyi har ya gano lauyan bogi ne inda ya kira ’yan  sanda suka kama shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa, a farkon watan Afrilu ne wanda ake zargin ya shiga komarsu. Ya ce binciken da suka faro ya tabbatar musu da cewa, lauyan bogin ya dade yana cin karensa babu babbaka, “Da wani ma’akacin gidan yari ya yi ido hudu da lauyan bogin ya gane shi ya kuma shaida mana a baya ma an taba kama shi a kan wannan laifin inda ya yi zaman kaso na wata 6,” inji shi.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bashir Maka, ya ba da umarnin ci gaba da binciken wanda ake zargin ya kuma ba da tabbacin gurfanar da shi a gaban kotu, ya ce rundunar ba za ta saurara wa batagari a jihar ba.