Lauyoyi 100 sun kalubalanci hukuncin korar Abba Gida-gida
Lauyoyi sama da 100 sun kalubalanci hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Tarayya na soke zaben Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Akalla lauyoyin sa-kai 100 ne suka kalubalanci hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Tarayya na korar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga ofis.
Lauyoyin, wadanda suka fito daga jihohin Arewacin Najeriya sun yi Allah-wadai da hukuncin wanda a cewarsu, cike yake da kurakurai.
Daya daga cikin jagororin lauyoyin,Barista Yusuf Ado Ibrahim, ya shaida wa taron ’yan jarida da suka gudanar a Kaduna cewa matsayinsu na lauyoyin sa-kai daga jihohin Arewa 19 suna goyon bayan Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Kano da talakawan jihar suka zaba.
“Don haka muna tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a kokarinsa na neman hakkinsa da ta mutanen Kano a Kotun Koli.
- Gwamnan Kano ya kama hadiminsa yana karkatar da abincin tallafi
- Muguwar kaddara ta sa na shiga Kannywood —Hafsat
“Dukkanmu da muka karanta hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kwanan nan mun ga kurakurai a shafuka 67, wanda hakan ke nuna akwai damuwa.
“Idan kuna kuskure ne kamar yadda suka fadi, toh gaskiya zai yi wuyar yafuwa.
“A matsayinmu na lauyoyi muna mutunta Kotun Koli, saboda haka muna kira gare ta da kada ta yarda bangaren zartaswa ta yi mata shisshigi wurin tabbatar da martabar bangaren shari’a” in ji shi.
Shi ma da yake amsa tambayoyi, daya daga cikin lauyoyin, Barista Usman Ashafa, ya ce a yanzu haka ’yan Najeriya musamman talakawa suna shakkun samun adalci a kotu a sakamakon abin da ke faruwa a Kano.
Ya ce a matsayinsu na lauyoyi, suna ganin akwai bukatar bangaren shari’a ya maido da mutunci da martabarsa a idon ’yan kasa, ta hanyar bai wa talakawa abin da suka zaba a Kano, wato Gwamna Abba Kabir Yusuf domin, a cewarsa, kowa ya san shi talakawan Kano suka zaba.
Ya ce a tun daga lokacin da aka yanke hukuncin ake ta samun zanga-zangar lumana a jihar wanda hakan ke nuna jama’a sun san hakkinsu da kuma abin da suka zaba kuma a shirye suke kare kuri’arsu.