Lauyoyi na taimakawa wajen jinkirin yanke hukunci – Umaru Abdullahi

Tsohon shugaban kotun daukaka kara, Mai shari’a Umaru Abdullahi, Walin Hausa, ya bayyana wa Aminiya cewa bai dace ana barin karamin mai laifi a gidan yari domin jiran shari’a ba, domin zai fito a matsayin babban dan ta’adda. Ga yadda hirar ta kasance:  Aminiya:Mene ne ra’ayinka game da furucin shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki […]

Lauyoyi na taimakawa wajen jinkirin yanke hukunci – Umaru Abdullahi
Lauyoyi na taimakawa wajen jinkirin yanke hukunci – Umaru Abdullahi

Tsohon shugaban kotun daukaka kara, Mai shari’a Umaru Abdullahi, Walin Hausa, ya bayyana wa Aminiya cewa bai dace ana barin karamin mai laifi a gidan yari domin jiran shari’a ba, domin zai fito a matsayin babban dan ta’adda. Ga yadda hirar ta kasance:

 Aminiya:Mene ne ra’ayinka game da furucin shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki na cewa hukuncin babban kotun koli ba ta yi masa dadi ba?
 Mai Shari’a: Duk dan Adam ba ya jin dadi idan abin da yake burin samu bai tabbata ba. Don haka ne ya fadi wannan magana cikin bacin rai, amma ba ni son in ce ya yi fushi. Haka harkar shari’a take, domin yawancin masu hasashe daga waje a harkar shari’a ba su da cikakken masaniya dangane da shari’ar ita kanta. Amma wadanda abin ya shafa su kadai ke da cikakkiyar masaniya dangane da me shari’ar ta kunsa dungurungun dinta. Ban ga laifinsa ba, don dan Adam ne, don yana da dama ya nuna damuwarsa. Masu shari’a sun yi aikinsu, kuma kila wata rana shi shugaban majalisar  ta dattijai ya yi murna da wata hukuncin ta shari’a a nan gaba. (Dariya)
Aminiya: Mene ne manufar kafa kwamitin amintattu (Unity Bar)?
 Mai Shari’a: Manufar ita ce don samar da fahimta tsakanin alkalai da lauyoyi a Abuja da kuma sauran jihohi gaba daya. Wannan zai taimaka wa harkar shari’a don su yunkura su yi aiki don rage matsalolin harkar shari’a. Lallai ba za a samu ci gaban kowace kasa ba in ba a gudanar da shari’a mai inganci.
Aminiya:Ta ya ya ne za a iya karrama masu shari’a wadanda suka rike gaskiya har zuwa lokacin da suka yi murabus?
 Mai Shari’a: Na kwashe kusan shekaru arba’in ina harkar shari’a kafin in ajiye aiki. Ban yi aiki don wani ya karrama ni ba, sai dai domin aikina na yi. Kuma ai duk wanda ya gyara ya sani, sannan wanda ya bata shi ma ya sani. Idan a cikin wannan lokaci wani ya ji dadin aikina ba laifi. Idan kuma a dalilin aikina wani ya ji bai gamsu ba, ban ga laifinsu ba ko da sun yi min batanci (dariya). Shawara ta ita ce alkali ya tsare gaskiya, sannan ya yi aiki daidai da dokar da aikinsa ta tanada, da kuma kula da rantsuwarsa ta aiki. Idan mai shari’a ya tsare wannan dokar, zai ji dadi. Amma duk wanda ya kawo son zuciyarsa, to mutum zai kasa barci domin bacin rai. Kada wani alkali ya damu da maganar ana yabonsa ko akasarin haka.
 Aminiya: Mene ne munufar Hukumar tantance aikin masu shari’a (JPER)?
Mai Shari’a:  Ina daya daga cikin jami’an Hukumar shari’a ta kasa (NJC) don tantance masu shari’a. Alkalan Najeriya suna kokari kwarai, duk da cewa wadansunmu ba su jin dadin yadda ake tafiyar da wasu shari’un a hali irin na dan Adam. Domin a duk inda mutane suke wasu suna da hazaka, wasu suna tsaka-tsaki, wasu kuwa kasalallu ne matuka. Duk inda ka samu irin wannan gamin-gambiza to akwai matsala. Misali shi ne, a watan Agustan da ya wuce, akwai alkalai dubu daya da ashirin a tsakanin babban kotun koli da babban kotun daukaka kara da manyan kotuna da na jihohi da na shari’a da kuma na gargajiya, watau wadanda muke ce masu manyan kotuna ke nan. Muna iya mizanin cewa a yanzu muna da alkalai 1,050, domin an nada wasu a kotunan daukaka kara na tarayya. Ba ina nufin ba gurbatattu ba, amma akwai na kwarai sosai a cikinsu.
Aminiya:Mene ne matsalolinsu?
Mai Shari’a: Matsolilin sun hada da illar da aka samu a harkar shari’a, wanda ya dace ne kowane alkali yana da kotun da yake shari’a a ciki da ofisi da dakin karatu da litattafai da akawu masu aiki karkashinsa. Domin ba a yin aikin alkalanci sai da ma’aikata, sannan wasu na da kwazo, wasu kuwa in ba ka kula ba sai su lalata maka aiki don kasala, domin magatakarda na iya yi maka kancal ta hanyar jera maka shari’u wadanda ba za ka iya kammala su a wuni guda ba. Idan haka ta faru, yaya za ka yi da sauran da ba a kammala ba?
 Sannan idan ka daga ranakun shari’ar to za su ci karo da wasu, har shari’un su yi yawa su zama alakakai. Domin idan an tsara za ka saurari shiri’u goma, amma ka yi uku kadai, domin za ka saurari lauyoyi, za ka yi rubutu, ai ka ga abin ba babu dadi. To irin haka ne ya sa wasu suke tsoma baki cewa alkalai ba sa yin aikinsu. Ya kamata su san cewa hakan yake sa alkali ya jingine yanke hukunci har sai ya yi bincike mai zurfi kafin ya yanke hukunci, don wadannan abin kula ne matuka. Amma ban ce babu alkali kasalallu ba, to wadannan su ke janyo harkar shari’a tana tafiyar hawainiya. Mutane daban-daban, har ma da lauyoyi da masu shigar da kara, sun yi sharhi cewa a inganta harkar shari’a, dalilin fito da wannan tsarin ke nan. Wannan ya sa hukumar NJC ta ce mafita ita ce a da lallai ne duk Alkali ya yanke hukunci har hudu a watanni uku. Sannan manyan alkalai su yanke shari’u biyu, don suna shari’a kuma suma kula da ma’aikata.
Aminiya: Ya harkar shari’a take  a kasashe da suka ci gaba?
Mai Shari’a: Wadannan kasashe suna da masu rubutu a na’ura mai kwakwalwa, sai dai alkali ya dan rubuta abin da ba a rasa ba, da yin aiki da na’urar kwamfuta. Ana yin yunkurin hakan, amma abin ya ci tura a nan. Don ganin a rage cinkoso a harkar shari’ da na masu jiran shari’a a gidajen fursuna ya sa muka kara yawan shari’un da Alkalai za su yanke zuwa shida a duk watanni uku. Haka yasa muka kafa cibiyar fahimta tsakanin Alkalai da lauyoyyi mai suna “Unity Bar”
 Aminiya: Mene ne laifin lauyoyi dangane da tafiyar hawainiyar shari’a?
 Mai Shari’a: Suna zuwa kotu ba tare da sun yi nazarin shari’a ba. Sai su nemi a dage shari’ar. Idan Alkali ya ce ba zai daga ba sai Lauya ya yi ta gunagunin an danne masa hakki. Wasu lauyoyin sai su je kare wadanda suke karewa a shari’u biyar a kotuna daban-daban a wuni guda. Amma akwai na kwarai da ke yin ayyukansu da inganci. Idan ya nemi a dage kara idan an yarda, to ran da za a shiga sai ya turo wani sabon lauya ma’aikacinsa shi ma sai ya ce ba a yi masa bayanin shari’ar ba. Ko kuma ya rubuto wasika cewa ba shi da lafiya, duk dai don neman a dage kara.
Aminiya: Ya kuke tsara aiki ga ma’aikata?
 Mai Shari’a: Muna kuma rubuta takardar jan kunne ga alaalai da suke yi wa aiki rikon sakainar-kashi. Idan aka sake ba da takardar jan kunne to idan an zo karin girma wannan alkali ba zai samu ci gaba ba. Idan kuma muka tuntubi shugaban kula da kotuna, musamman a jihohi, sai ya ce suna da karancin kayan aiki da kudi, inda har sai sun je sun yi maula a wurin gwamna, wanda hakan bai dace ba.