Lauyoyin Kano sun maka Ado Gwanja da Safara’u a kotu kan lalata tarbiyya

An maka wasu fitattun mawakan zamani da jaruman kafar TikTok na Arewacin Najeriya a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano bisa zargin bata tarbiyya.

Lauyoyin Kano sun maka Ado Gwanja da Safara’u a kotu kan lalata tarbiyya

An maka wasu fitattun mawakan zamani da jaruman kafar TikTok na Arewacin Najeriya a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano bisa zargin bata tarbiyya.

Wadanda aka zayyana a wasikar da aka aika wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano sun hada da Ado Gwanja da Sanusi Oscar 442 da Safiya, wadda aka fi sani da Safara’u.

Aminiya ta samu kwafin wasikar da kotun Shari’ar Musulunci da ke zamata a Bichi, Jihar Kano ta rubuta wa ’yan sanda na neman a binciki koke-koken da ke masu gabatar da kara.

Sauran sun hada Dan Maraya da Amude Booth da Kawu Dan Sarki  da Ado Gwanja, da Murja Kunya, da Ummi Shakira, da Samha Inuwa da kuma Babiyana.

Takardar wacce magatakardan kotun, Aminu Muhammad ​​ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, “Alkalin Kotun, Mai shari’a Dokta Bello Musa Khalid ya umurce ni da in rubuta tare da neman ku gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin domin daukar matakin da ya dace.”

Wasu majiyoyi sun ce ana zargin wadanda ake kara ne bisa laifuffukan da suka hada da wakokin rashin tarbiyya da rawar Tiktok masu alaka da lalata tarbiyyar al’umma.

Tunda farko wasu lauyoyi ne suka shigar da karar gaban kotun wadanda suka hada da Muhd ​​Ali Hamza  da Abba Mahmud da Sunusi I. Umar da Abba, A.T Bebeji Esq, da B.I Usman Esq, da Muhd ​​Nasir Esq da L.T Dayi Esq da G.A Badawi da Badamasi Suleiman Gandu Esq.