Layi a gidajen man fetur
‘yan Najeiya sun wayi gari a makon da ya gabata suka ga dogon layi a gidajen man fetur, wanda ya nuna alamun rashin mai, kuma ya mayar da hannun agogo baya na wahala da rashin tabbas. Lamarin ya zo wa ‘yan Najeriya da ba-zata, domin a tunaninmu, matsalar rashin man fetur ya zama tarihi saboda […]
‘yan Najeiya sun wayi gari a makon da ya gabata suka ga dogon layi a gidajen man fetur, wanda ya nuna alamun rashin mai, kuma ya mayar da hannun agogo baya na wahala da rashin tabbas. Lamarin ya zo wa ‘yan Najeriya da ba-zata, domin a tunaninmu, matsalar rashin man fetur ya zama tarihi saboda yadda aka dade ana samunsa. Amma kuma wannan rashin man ya samo asali bisa rade-radin da ake samu na cewa za a bara kudin mai. Wannan ne ya janyo wahalar samun man, wasu gidajen man kuma suka fara boye man domin tsammanin gwamnati za ta bara kudi.
bungiyar ‘yan kasuwan man fetur masu zaman kansu (IPMAN), barbashin jagorancin sakatarensu na basa, Danladi Pasali sun fada bayan wani zama da suka yi da Hukumar NNPC cewa wasu daga cikin masu gidajen man suna amfani da yadda ake neman man saboda yanayin lokacin da ake ciki na bukukuwa domin su bullo da wani irin wahalar man na wucin gadi.
Kwamitin Majalisar Dattawa a kan albarkatun man fetur ta ce za ta yi wani bincike a kan gidajen man basa baki daya, sannan kuma ta ce ta bubaci Hukumar NNPC ta ba kwamitin abin da take rabawa gidajen mai a kullum.
A daidai lokacin da ake ciki na rade-radi da rashin tabbas, ba tare da wani bwbbwaran bayani ba daga gwamnati. Minista a ma’aikatan albarkatun man fetur, Dokta Ibe Kachikwu a ranar da Alhamis ya ce abin da ya janyo rashin man fetur din da ake gani yanzu shi ne yadda man fetur din ya yi baranci. Amma sai ya ce Hukumar NNPC tana bobarin ganin cewa ta magance matsalar rashin man na ba da dadewa ba.
“Babbar matsalar ita ce rashim albarkatun man fetur din da yawa. Saboda Hukumar NNPC ce kadai ke shigo da man fetur zuwa basar baki daya,” inji shi. Ya ce akwai ma’adana mai girma da aka ajiye domin man da aka shigo da shi, sannan ya bara da cewa ana yin duk mai yiwuwa wajen ganin cewa an samu man fetur din a lokacin bukukuwan da ke gaba da kuma sabon shekara. Ya ce man jiragen ruwa guda hudu za su kawo man fetur kwanan nan, sannan kuma jiragen sama guda 20 suna tafe.
A daya bangaren kuma, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a game da yiwuwar bara farashin man fetur, babban manajan Hukumar NNPC, Maikanti Barau cewa ya yi babu wannan maganar, “Ba a bani umarni in bara farashin mai ba: Ko wancan barin da aka yi sai da Hukumar kula da farashin ta bada shawara,” inji shi.
Duk da cewa ‘yan kasuwan man fatur da wasu masu ruwa da tsaki suna yawan amfani da lokutan Kirsimeti domin samun riba mai yawa ta hanyar buntata wa mutane, musamman matafiya, a wannan lokacin muna so gwamnati ta fito fili ta yi bayani idan har da gaske ne tana so ta bara farashin man fetur, duk da bayanin da Maikanti Baru ya yi.
Abin kunya ne da takaici a ce Najeriya, wadda basa ce mai albarkar man fetur sai ta dogara da wasu basashen waje domin tace mata man fetur, sannan a dawo da shi Najeriya kafin a yi amfani da shi. Gidajen man mu ba sa aiki, sannan kuma an gaji da jin cewa gwamnati za ta gyara su ba tare da wani abin a zo a gani ba. Don haka ya kamata gwamnati ta yi da gaske wajen tace mana man fetur dinmu, ba wai ta zauna tana jiran ‘yan kasuwa su bude matata man fetur din ba, domin wannan zai magance matsalar ne kawai na dan lokaci kadan.
Da a ce matatun man fetur din suna aiki yadda ya kamata, da ba za mu shiga wannan matsalar ba. Ya kamata gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da man fetur. Mutanen basar nan sun gaji da zama cikin tsammani a sanadiyar wasu ‘yan tsiraru mutane daga cikin gwamnati ko ‘yan kasuwa ko kuma bungiyoyi saboda son kai ko rashin aiki yadda ya kamata. Ya kamata a gane cewa rashin man fetur ya wuce maganar ababen hawa kawai, domin yana shafar dukan bangarorin rayuwa, domin wasu suna amfani da shi a janareto a gidajensu da wajen sana’o’insu. Don haka, rashinsa, ko da kuwa da gangan aka kawo rashin ko akasin haka, zai kawo cikas ga bangarori da yawa na rayuwa ba wai bangaren sufuri ba kawai.