Layin karbar abincin Mariya: Taimako ko kashe zuciya?

Ana dafa akalla katan 500 na taliya a lokaci guda; Wasu na ganin ciyarwar na iya haifar da matsala a cikin al’umma

Layin karbar abincin Mariya: Taimako ko kashe zuciya?

Layin karbar abincin sadaka da Hajiya Mariya. (Hoto: Lubabatu I. Garba)

Fatima wata baiwar Allah ce da ke zaune a Unguwar Dabai a wajen birnin Kano – galibin mazauna yankin talakawa ne wadanda sai sun yi buge-buge suke samun abin sakawa a bakin salati.

Da ganin ta ka san cewa ta dade ba ta yi sabon dinki ba domin kuwa atmafar da ke jikinta duk ta kode; alamun cewa tana cikin halin matsi.

Kusan shekara biyu da suka wuce Fatima ta wayi gari nauyin iyalinta ya dawo kanta.

A bisa al’ada, musamman a kasar Hausa, maigida ne kan dauki nauyin matarsa da ’ya’yansa, amma a wancan lokacin, abin da ya bayyana ga Fatima shi ne mijinta ba zai iya ci gaba da daukar alhakin ciyar da ita da ’ya’yansu ba, balle ya biya musu wasu bukatu.

Saboda haka ne ya zama dole a kanta ta nemi wasu hanyoyin da za ta bi ta samo musu mafita.

“Kin san yanayin da ake ciki – magidanta sun zama sai a hankali; haka suke ficewa daga gida su bar mu.

“Mu kuma ya zama dole mu fita mu nemi abin da za mu ba yaran”, inji Fatima.

Domin biyan bukatunsu na yau da kullum – wadanda ba na abinci ba – Fatima ta fara sana’ar wankau, tana shiga makwabta ta karbo kayansu masu dauda ta wanke a biya ta.

Amma kafin ta fara wankin, a kullum takan yi wata dabara ta samo musu abinci ba tare da ta kunna wuta ko ta yi nika ko markade ba.

Wa ya ki sauki?

Sau biyu a kowace rana Fatima kan yi tafiyar kasa ta kusan kilomita daga unguwarsu zuwa bakin titi inda za ta hau keken A Daidaita Sahu ta biya akalla N100 a kai ta Kofar Mazugal.

Da yake takan taho da daya daga cikin ’ya’yanta ne, takan biya N200 ke nan.

Daga nan kuma za ta sake takawa zuwa Unguwar Koki, gidan Hajiya Mariya Dantata, inda za ta karbi dafaffen abincin sadaka.

“Hakan [abu ne] mafi sauki a gare ni [a kan] a ce ni zan nemo abin da zan ciyar da kaina da ’ya’yana…

“Tun da muka samu wanannan wurin wallahi ba mu da wata matsala, domin ina samun isasshen abincin da muke ci tare da yarana.

“Kai wallahi wani lokacin ma har sai na ba wasu,” inji ta.

Sukan taho ne da wani babban bokiti wanda da safe akan cika musu shi da shayi ko koko a kuma ba su burodi; da yamma kuma duk irin abincin da aka dafa.

Abincin Olala

“Olala” shi ne sunan da wasu kan kira dafaffen abincin da Fatima ke zuwa karba.

Abincin sadaka ne wanda ake raba wa almajirai da attajirar nan kuma mahaifiyar attijirin Afirka Alhaji Aliko Dangote, wato Hajiya Mariya Sanusi Dantata ke daukar nauyin dafawa.

Abinci ne da ake ciyar da dubban almajirai ko mabukata a Jihar Kano a kullum.

Ana raba abincin ne a cibiyoyin rarraba dafaffen abinci na Hajiya Mariya wadanda suka hada da kofar gidanta da ke Unguwar Koki da kuma gidanta da ke Unguwar Bachirawa. Sai kuma makarantun da tsangayun Alkur’ani.

Akwai kuma asibitoci, wadanda suka hada da Asibitin Masu Ciwon Fata da ke Bela da Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da Asibitin Masu Tabin Kwakwalwa da gidajen gajiyayyu da sauransu.

Binciken Aminiya ya gano cewa an shafe tsawon shekara 40 Hajiya Mariya tana yin wannan abinci na sadaka ga mabukata ba tare da fashi ba.

Layin masu karbar abincin sadaka a gidan Hajiya Mariya Dantata. (Hoto: Lubabatu I. Garba).

Taliya katan 500 kullum

Wani daga cikin ma’aikatan gidan wanda ya nemi a boye sunansa ya ce, “Kin ga a cikin gidan nan muna da tukwane sama da 70.

“Sannan a can Bachirawa ana da tukwane 15. Haka kuma ana dafa wani abincin a gidajen wasu ’yan uwan Hajiya – ana dafa kimanin tukwane 15 a kowane gida.

“A duk ranar da za a dafa taliya, ana dafa kimanin katan 500. Haka ita ma fulawa ana amfani da mota guda wajen yin alkubus.

“Haka kuma gero da ake yin koko da shi da sukari. Shi ma burodi ana kawo mota guda don rabawa ga mabukata,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Baya ga kayan miya da ake kawowa mota guda, a gefe guda kuma a kullum ana yanka shanu wani lokaci ma har da raguna don yin amfani da su a girkin.”

Game da kiyasin mutanen da ke karbar sadakar abincin ya ce babu wanda zai iya bayyana yawansu lura da cewa ba kawai almajirai ne ko gajiyayyu ke amfana ba har ma da mutanen gari wadanda ba su da karfin aljihu.

“Magidanta sun fi yawa wajen karbar abincin; wadanda kuma yawancinsu za ki iske suna da iyali.

“Kin ga kuwa Allah ne kadai Ya san yawan mutanen da suke cin wannan abinci,” inji shi.

Matsin tattalin arziki

Majiyarmu ta bayyana cewa saboda halin matsin tattalin arziki da aka shiga a wannan lokaci, yawan masu karbar abincin karuwa yake yi a kullum; lamarin da ya janyo abincin ba ya isa kamar da.

“A ’yan shekarun baya lokacin abubuwa ba su zama haka ba, za ka samu mutanen da ke karbar abincin nan almajirai ne na hakika.

“Amma saboda halin kunci da al’umma suka shiga, mutanen gari ma karbar abincin suke yi.

“Ni na tabbata da za a tsaya a tantance, to mutanen garin da ke karbar abincin sun fi almajiran yawa.

“A kullum kuma yawansu karuwa yake yi. Shi ya sa ma a wani lokacin za ki tarar abincin ba ya isar su, duk da cewa masu kula da dafa abincin sukan yi kokarin kara yawan abincin a koyaushe,” inji majiyar.

Wani magidanci wanda ya ce kullum yana zuwa ne daga Unguwar Gwale, ya jaddada hakan.

“Wallahi yanayi ne. Tun ina iya kai abinci gidana har ya zama ba ni da abin da zan iya ba su.

“Hakan ya sa nake zuwa nan kullum karbar abincin sannan in kai wa iyalina su ci,” inji shi.

Wani almajiri da ke karbar abincin a Unguwar Bachirawa mai suna Musa Sani kuwa cewa ya yi a yanzu haka shi da iyalinsa gaba daya sun dogara ne kacokan a kan wannan abincin sadaka.

“Kuma yana isar mu. Idan gari ya waye ma nan zan zo in karbi koko da burodi. Idan muka karya, to wannan ragowar burodin shi ake ajiye wa kananan yara a matsayin abin da za su ci da rana.

“Mu kuwa manyan ba mu sake sa rai da wani abincin sai yamma idan mun karbi irin wannan abinci,” inji shi.

‘Olala ya fi abincin wasu attajiran’

Ko da yake bukatar ciyar da iyali ce ta tilasta mata zuwa karbar Olala a kullum, Fatima ta ce abincin yana kuma jin hadi.

“Wannan abinci ko a gidan mutum sai haka. Na tabbata wannan abincin ya fi na gidajen attajirai da yawa dadi domin abinci ne da namansa a ciki.”

Ita ma wata almajira mai suna Hafsatu Ado, wacce ta ce tana zuwa daga Rijiyar Lemo don karbar abincin, ta ce “Ke ma shaida ce. Kin ga irin abincin da ake ba mu wanda ko a gidanka sai haka.

“Wannan mata sai dai mu yi mata addu’ar cikawa da imani kawai.”

Shi kuwa wani magidanci ya ce abin da ke burge shi da abincin sadakar shi ne yadda duk girman mazubin da mutum ya kai za a cika masa shi.

‘Abincin ya hada zumunci’

Wata mai suna Halima ta ce sakamakon shafe tsawon shekaru suna karbar abinci a kofar gidan Hajiya Mariya, a yanzu har sun kulla zumunci da wasu.

“Kin ga dai harkar karbar abinci ce take kawo mu nan, amma a yanzu mun zama ’yan uwa da wasu da dama.

“Muna zumunci idan wani sha’ani ya tashi mukan je wa juna don yin murna ko jajantawa,” inji ta.

Da dama daga cikin mutanen da kan je karbar abincin, musamman almajirai, sun yi zargin cewa jami’an tsaron da ke wurin kan ci zalinsu.

Wadannan almajirai sun ce jami’an na bin su da zagi da ma duka.

Sai dai jami’an sun musanta hakan da cewa suna rike da bulala ne kadai don tsoratarwa.

Layin almajirai masu karbar abincin Sadaka da Hajiya Mariya ke bayarwa. (Hoto: Lubabatu I. Garba).

Sai dai kuma…

Sai dai a daidai lokacin da masu karbar wannan sadaka suke yaba wa Hajiya Mariya, wasu mutane kan yi suka a kan yadda ake tara almajirai da mabukata da sunan ba su sadakar abinci.

Yayin da wasu suke ganin cewa hakan zai haddasa wa masu karbar sadakar mutuwar zuciya, wasu kuma na ganin da ka bai wa mutum kifi kullum gara ka koya masa yadda ake kama kifi – ma’ana da sana’a Hajiya Mariya ta koya wa wadannan mabrata ko ta ba su ayyukan yi don iya tsayuwa da kafafunsu da ya fi.

Malam Aliyu Haruna, Limamin Masallacin Juma’a na Ibn Ya’akub da ke Unguwar Salanta a Kano, ya ce ciyarwa abu ne mai kyau a Muslunci, amma fa kamata ya yi a rika sara ana duban bakin gatari.

“Babu shakka akwai lada a cikin wannan aiki na ciyarwa, sai dai kuma zai iya gadar da wata matsala wadda za ta dami al’umma wadda kuma ba ita Musulunci yake nema ba.

“Irin wadannan abubuwa su suka jawo mana halin da muka samu kanmu na barace-barace da sauransu”, inji shi.

Yayin da yake nuna rashin dacewar mutum ya dogara kacokan da wani mutum, Malam Aliyu ya kara da cewa Musulunci ya zaburar da mutane a kan neman na kansu.

Shiga daji debo itace

“Shi Addinin Musulunci abu ne da yake da tsari, don haka komai mutum zai yi akwai tsari.

“Za a duba me Alkur’ani ya ce, me Hadisi ya ce, a kan wani al’amari saboda duk abin da za a yi ya kamata ya zama akwai tsari ba kawai a yi shi haka nan kara zube ba.

“Misali, idan za a yi wani abu na taimako akwai gidajen marayu a unguwanni wadanda an san su ba su da halin samun abinci ko kuma wasu wurare da aka killace masu rauni, to irin wadannan mutane suna bukatar taimako babu laifi idan an taimaka musu,” inji shi.

Limamin ya kuma ce, “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zaburar da al’ummarsa a kan neman na kansu.

“An ruwaito shi yana cewa, ‘Dayanku ya tashi ya je daji ya yi itace ya je ya sayar ya fi ya je ya roka a ba shi’.

“Idan har za a ajiye wasu mutane ana ba su abinci a kullum to zai iya zama kamar ana ce wa mutum kada ka je ka nema ne musamman a wannan lokaci.”

Mutuwar zuciya

Khalifa Mustapha Dankadai mai sharhi ne a kan al’amuran yau da kullum, kuma mai fafutukar inganta rayuwar almajirai, wanda yake ganin al’umma ta bar jaki tana dukan taiki.

“Abin da ya dace da rayuwar almajirai shi ne a fitar da tsarin da zai kawo gyara a rayuwarsu ta hanyar inganta ta da kuma samun dorewar shi.

“Tallafi ko ciyarwa, duk da cewa abu ne mai kyau, idan aka dade ana yi to zai kashe zuciyar wanda ake ba wannan tallafin.

“Kuma ba abu ne da ya fiye dorewa ba domin da zarar wanda yake bayar da wannan tallafi ba ya nan to shi ke nan komai ya tsaya cak.

“Da za a ce a maimakon wannan ciyarwar da wata cibiya aka samar wadda za a rika koya wa wadannan mutane sana’o’i tare da tallafa musu da jari don su dogara da kansu to da shi zai fi.

Manyan robobi da ake daukar abincin Hajiya Mariya domin kaiwa wuraren da ake rabawa sadaka. (Hoto: Lubabatu I. Garba).

“Idan ya so a danka harkar kula da lamarin ga wata kungiya mai zaman kanta wadda za ta rika bibiya tare da kula da yadda lamuran ke tafiya”, inji shi.

Mun yi yunkurin jin ta-bakin Hajiya Mariya game da wannan lamari, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.

Da muka tuntubi was daga cikin mutanen da ke kusa da ita sun shaida mana cewa ba ta hira da ’yan jarida, sannan su kansu sun ki cewa uffan a madadinta.

Yayin da rayuwa take kara afkawa cikin matsi dai akwai yiwuwar layin da ake yi a wuraren rabon Olala zai ci gaba da karuwa – sai dai idan mawadata a cikin al’umma za su saurari shawarar malamai da masu fafutuka, su samar da cibiyoyin koyar da sana’a da bayar da tallafin jari ga mabukata.